Dan Najeriya Ya Yi Amfani Da GB Whatsapp Wajen Kama Budurwarsa Da Ke Cin Amanarsa, Ya Fallasa Hirarta

Dan Najeriya Ya Yi Amfani Da GB Whatsapp Wajen Kama Budurwarsa Da Ke Cin Amanarsa, Ya Fallasa Hirarta

  • Wani mai amfani da Twitter ya shawarci mutane da su ci gaba da jin tsoron kaidin mata yayin da ya yada hirar budurwarsa da wani saurayinta
  • Budurwar ta shirya hadadden sako zata aikawa saurayinta na ainahi amma sai ta yi kuskure ta aikawa daya saurayinta
  • Sai dai ta goge sakon, amma bai bar wajan saurayin ba saboda yana amfani ne da GB Whatsapp

Wani dan Najeriya ya yi amfani da daya daga cikin amfanin GB Whatsapp wajen kama budurwarsa da ke cin amanarsa.

Wani mai amfani da Twitter mai suna @only1Ayoo ya yada hirar da ya gudana tsakanin budurwar maciya amana da saurayinta, yana mai bukatan zama da kada su daina jin tsoron mata.

Hoton mace da namiji da kuma sako
Dan Najeriya Ya Yi Amfani Da GB Whatsapp Wajen Kama Budurwarsa Da Ke Cin Amanarsa, Ya Fallasa Hirarta Hoto: Klaus Verdfelt, Jasmine Merdan, Twitter/@only1Ayoo
Asali: Getty Images
"Baaaba, idan ka wayi gari da safen nan sannan ka daina jin tsoron mata ga tuni a nan don ka ci gaba," @only1Ayoo ya rubuta.

A hirar, budurwar mai suna Amaka ta shiryawa ainahin saurayinta mai suna Deji daddadan sako a ranar zagayowar haihuwarsa sannan ta aikawa kawarta a Whatsapp don ta duba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abun takaici a gareta, sai ta yi kuskuren aikawa daya saurayinta sannan ta goge sakon a lokacin da ta lura da hakan.

Godiya ga tsarin GB Whatsapp, bata iya ta goge sakon daba dukkanin bangarorin ba kuma hakan yasa daya saurayin ya gano cewa ba shi kadai ne a cikin rayuwarta ba.

Sai dai kuma ta ba da hakuri cewa sakon na wata kungiyar yan ajinsu ne, amma bai yarda ya fada a tuggun karyarta ba.

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Echelon26120 ya ce:

"Haka na yi gaba da sakon wata zuwa gareta dauke da taken. Dan uwa kalli wannan, zan yi wasa da hankalinta kamar yadda na saba sannan na rabu da ita idan ta fola. A takaice dai na rasa ta. Na san irin wannan kuskuren."

@ibsudais ta ce:

"Idan haka ne me zai sa yayi fushi? wannan sakon na wanda take cin amana da shi ne amma sai ta so turawa kawarta don jin ra'ayinta a kai kafin ta tura sannan tayi kuskuren turawa saurayinta. kun gane yan zu?"

@seunney_ ya ce:

"Wasu matan dai basu da kunya."

Yar baiwa: Yadda karamar yarinya ta burge mutane da kwazonta

A wani labarin, wata karamar yarinyar yar watanni 19 ta sace zukatan jama'a a soshiyal midiya bayan bayyanan wani bidiyonta mai ban mamaki.

Duk da karancin shekarunta, yarinyar dai ta kawo sunayen manyan biranen kasashen duniya tsaf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel