Yadda Shugabannin Ma'aikatun Gwamnati A Nigeria Suka FI Shugaban Kasa Daukar Albashi

Yadda Shugabannin Ma'aikatun Gwamnati A Nigeria Suka FI Shugaban Kasa Daukar Albashi

  • Hukumar tattara kudaden shiga da kuma kasafin kudi (RMAFC) ta ce wasu ma’aikatan gwamnati na samun albashi fiye da na shugaban kasa Muhammadu Buhari.
  • Shugaba Muhammadu Buhari Ya Amince Da Gyarawa Tare Da Karawa Ma'aikatan Shari'a Albashi
  • Har Yanzu Akwai Jihohin Da Basu Kaddamar Da Tsarin Biyan Mafi Karancin Albashi na Naira 30,000 Duk Wata

Shugaban Hukumar tattara kudin shiga a Nigeria yace albashin shugaban kasa bai kai N1,300,000 a wata ba. Ciki kuwa har da duk da alawus din shugaban kasa a cikin albashin.

Shugaban wanda yai waiwaye yace a shekarar 2008, an dauki wannan a matsayin babban kudi amma yanzu, akwai mutane a kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati wadanda suke samun ninki biyu, uku, ko ma hudu, na abinda Buharin ke dauka.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

Shugaban RMAFC, Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a zantawarsa a gidan talabijin na Channels Television na Sunrise Daily a ranar Alhamis.

Suwaye Suka Fi Buhari Albashi

Shehu ya ce wasu ma’aikatan hukumomin gwamnati kamar hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), da babban bankin Najeriya (CBN), da dai sauransu, suna samun albashi da yafi na Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhariiii
Yadda Shugabannin Ma'aikatun Gwamnati A Nigeria Suka FI Shugaban Kasa Daukar Albashi
Asali: UGC

Rukunin Albashi daban-daban 17?

A cewarsa, Najeriya na da kusan nau'ikan albashi daban-daban guda 17 a fadin hukumomi da dama.

Don haka na ke bayar da shawarar a daidaita tsarin albashin ma’aikatan gwamnati, inda ya ce babu wani jami’in gwamnati da ya isa ya samu albashi fiye da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Shugaban Jam'iyyar APC Gidan Gyaran Hali Kan Laifi Daya

“Abin da nake cewa shi ne, babu wani ma’aikacin gwamnati da ya isa ya samu albashi fiye da na shugaban kasa amma muna da ma’aikatan gwamnati da suka fi shugaban kasa albashi: kamar irin su NCC, NIMASA, NPA, CBN” inji shi.

Shugaban RMAFC ya kuma ce wasu jami’an gwamnati suna samun N500m a matsayin kudin sallamar su amma Shugaban kasa yana samun N10m bayan wa’adinsa.

Bugu da kari, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumarsa za ta aiwatar da aikin sake duba albashin jami’an shari’a tare da sake duba albashin jami’an gwamnati domin nuna halin da ake ciki na zamantakewa da tattalin arziki.

Da aka tambaye shi ko gwamnati za ta iya biyan albashi a halin yanzu, sai ya koka da halin da wasu hukumomin gwamnati ke kashe duk kudaden da suke samu.

Yana mai cewa akwai kudaden shiga har Naira Tiriliyan 7 da ba a ajiyesu ba musamman awasu hukumomin. Don haka ya baiwa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati Ta’annati (EFCC) aikin bibiyar hukumomin da abin ya shafa.

Shehu ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da kudirin hada wasu ma’aikatu da ma’aikatu dan gudanar da ayyukasu a matsayin hanyar rage kudin gudanar da mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida