‘Ya ‘yan NNPP Sun Yi Mata Zanga-Zanga, Sun Bukaci a Canza ‘Dan Takara Kafin Zabe

‘Ya ‘yan NNPP Sun Yi Mata Zanga-Zanga, Sun Bukaci a Canza ‘Dan Takara Kafin Zabe

  • Abubuwa ba su tafiya daidai a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai alamar kayan dadi
  • A reshen jihar Kaduna, wasu ‘yan jam’iyyar adawar sun koka da takarar Suleiman Othman Hunkuyi
  • Akwai masu ganin Sanata Suleiman Hunkuyi ba zai iya kai NNPP ga nasara a zaben Gwamna ba

Kaduna - Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar NNPP a jihar Kaduna, sun yi zanga-zanga saboda ba su goyon bayan Suleiman Othman Hunkuyi.

Rahoton Daily Nigerian ya nuna wadanda suka yi zanga-zangar sun koka cewa Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ba zai iya lashe zaben Gwamna ba.

Najib Zakari mai neman kujerar ‘dan majalisar dokoki a mazabar Chikun, yace zaman Suleiman Hunkuyi ‘dan takarar Gwamna ya raba kan NNPP a jihar.

Hunkuyi zai kashewa NNPP kasuwa?

"Zaman Hunkuyi ‘dan takara ya jawo rashin hadin-kai tsakanin shugabannin jiha da na kananan hukumomi da kuma sauran ‘yan takara.

Mutane da yawa suna ganin bai da farin jinin da ake bukata domin jam’iyya ta lashe zaben 2023, wasu suna ganin zai saida takararsa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama’a da-dama sun yi niyyar shigowa jam’iyyar, amma suka fasa saboda shi.

- Najeeb Zakari

‘Ya ‘yan NNPP
Rabiu Musa Kwankwaso da Suleiman Othman Hunkuyi Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Kamar yadda aka rahoto Najib Zakari yana fada, takarar tsohon Sanatan za ta gogawa duk ‘yan takaran jam’iyyar NNPP bakin jini a zabe mai zuwa.

Har Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban kasa jam’iyyar hamayya ta NNPP zai gamu da cikas saboda Sanata Hunkuyi, a cewar Najib Zakari.

Inda matsalar take - Dogarawa

Shugabar mata ta jam’iyyar NNPP a karamar hukumar Sabon Gari, Habiba Abdullahi Dogarawa, ta zargi ‘dan takaran da rashin tafiya da sauran ‘yan jam’iyya.

Habiba Abdullahi Dogarawa tana ganin akwai laifin wasu na-kusa da Sanata Hunkuyi wadanda suke neman kawo karshen jam’iyyarsu ta NNPP.

People Gazette ta rahoto cewa Magaji Kurmin-Mashi yana da wannan ra’ayi, yace ya kamata a shugabanni su dauki mataki tun kafin lokaci ya kure masu.

Ba haka ba ne

Shugaban jam’iyyar NNPP na mazabar Samaru a karamar hukumar Sabon Gari a Kaduna, Umar Farouk Barau ya musanya wadannan zargi da suke yawo.

Umar Farouk Barau yace an yi ta bijiro da irin wadannan batu a baya, amma an dinke barakar.

Da Legit.ng Hausa ta tambaye shi ko Suleiman Othman Hunkuyi zai iya doke jam’iyyun APC, PDP da LP a 2023, sai yace Idan Allah ya so, haka za ayi.

Ana yi wa Tinubu sharri Inji APC PCC

An ji labari APC tace ana yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sharri musamman a Arewa cewa a lokacinsa za a sake maida Legas ta zama birnin tarayya.

Bayo Onanuga yace wasu na neman bata ‘dan takaran APC, ya tabbatar da cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta dauke birnin tarayya daga garin Abuja ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel