Tashin Hankali: An Bindige Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

Tashin Hankali: An Bindige Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

  • Wasu mutane ɗauke da Bindiga da ba'a san ko su waye ba sun harbe wani fitaccen mawaki har lahira a jihar Anambra
  • Bayanai sun nuna cewa mawakin kuma marubuci, Slami Ifeanyi, ya rasa ransa ne yayin da yake tuƙa sabuwar motar da ya siya a Awka
  • Wani aminin abokinsa yace duk da basu san dalilin kashe mawakin ba amma alamu sun nuna shiryayyen tuggu ne

Anambra - Wani fitaccen mawaki kuma marubucin waƙa a Najeriya, Slami Ifeanyi, ya gamu da ajalinsa a Umubere, yankin Awka, babban birnin jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Mawaƙin ɗan asalin jihar Anambra ya rasa ransa ne yayin da wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko suwaye ba suka harbe shi har lahira.

Slami Ifeanyi.
Tashin Hankali: An Bindige Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa Mawakin ɗan kimanin shekara 31 a duniya na cikin tafiya a sabuwar motar da ya siya sa'ilin da maharan suka farmake shi kuma suka kashe shi.

Kara karanta wannan

Ba Zan Daina Faɗa Wa Shugabanni Gaskiya Ba Komai Ɗacinta, Sarkin Musulmi

Wani abokin mawakin kuma amininsa, wanda ya ɗan yi tsokaci kan lamarin, ya yi zargin cewa harin da aka kai wa Marigayin wani tuggu ne aka shirya masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yana cikin tafiya yana tuƙa sabuwar Motar da ya siya makonni biyu kacal da suka shige lokacin da mummunan lamarin ya rutsa da shi."

"Duk da har yanzun ba mu gano dalilinn da yasa aka kai masa harin ba amma lamarin na da sarakaƙiya, ya nuna alamun dama shi aka nufa, harin shiryayye ne,' inji shi.

Marigayi Slami ya kasance kwararren mawaki a Najeriya, wanda ya yi fice wajen ba da nishaɗi da sauti mai zaƙi, yana amfani da baiwar da Allah ya ba shi wajen nishaɗantar da masoyansa.

Leadership tace Baya ga waƙa da yake yi, Slami ya kasance abin kwatance, jarumin Fim kuma shi ya kafa Kamfanin Slami Empire, wanda ya shirya gasar Anambra Got Talent.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Tayi Bayani a Kan Wahalar Abincin Da Ake Cewa Za Ayi a 2023

Yan Ta'adda Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Wani Gwamna Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma 'Yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar yan awaren IPOB ne sun yi barazanar tilasta wa gwamna ya yi murabus

A wani sakon murya da ya yaɗu, an ji wani da ya kira kansa kwamandan wani yanki na cewa tun da gwamnan Anambra ya zaɓi farautarsu da jami'an tsaro to zasu hana ya mulki jihar.

Haka zalika ya yi baranazar cewa zasu kai hari Asibitin wani Likita kuma zasu hallaka kowa suka taras idan har Likitan bai basu haɗin kai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel