Ba Zan Daina Fada Wa Masu Mulki Gaskiya Ba, Sarkin Musulmi

Ba Zan Daina Fada Wa Masu Mulki Gaskiya Ba, Sarkin Musulmi

  • Mai alfarmaki Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar, yace zai ci gaba da faɗa wa shugabanni gaskiya duk ɗacinta
  • A wurin taron Lakcar cikar Dr. Abubakar Olusola Saraki shekaru 10 da Rasuwa, Sultan yace ya san wasu basu son a gaya musu gaskiya
  • Basaraken ya bayyana cewa kowane shugaba zai amsa tambayoyi ranar Alkiyama kan yadda ya gudanar da mulkinsa

Abuja- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya sha alwashin cewa ba zai gaji da gaya wa masu rike da madafun iko gaskiya ba duk da ya san haka ba zai wa wasu daɗi ba.

Channesl tv ta tattaro cewa Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wurin Lakcar tunawa da Dakta Abubakar Olusola Saraki karo na 10 a Abuja ranar Litinin.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.
Ba Zan Daina Fada Wa Masu Mulki Gaskiya Ba, Sarkin Musulmi
Asali: Facebook

Sultan ya roki shugabanni su riƙa ɗaukar shawarin da yake basu a matsayin wani bawan Allah wanda ya damu da yanayin rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Bindige Wani Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

Sarkin, wanda ya jagoranci bikin Lakcar mai taken, "Mahawa kan shugabanci da mabiya," yace masu shirya Lakcar sun zaɓi batu mai muhimmmanci duba da kakar zaɓen da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan lamarin famin ciwo ne, gaskiya ce kaɗai zata masa magani. Muna bukatar gaya wa jagororin mu gaskiya, wasu lokutan idan ka faɗi gaskiya ba zata wa wasu shugabannin daɗi ba amma ba zamu daina ba."
"Duk lokacin da muka gaya musu gaskiya, su ɗauketa a matsayin shawari daga wasu mutane da suka damu da abubuwan dake faruwa da al'ummar da Allah SWT ya basu amana."
"Ku yi kokarin sauke nauyin haƙƙin da Allah ya ɗora muku a duniya saboda a ranar Lahira zai tambayeku, me kuka yi lokacin da na baku shugabanci? Kai kaɗai zaka amsa ba mai taimakonka."

- Sarkin Musulmai.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Kara Fitowa, Jami'ar FUD Ta Yi Magana Kan Kama Ɗalibinta Da Ya 'Zagi' Aisha Buhari a Twitter

Sarkin Musulmin ya shawarci kowane shugaba ya tsaya kan gaskiya, kana ya roke su da su zama masu gaskiya da adalci ga talakawansu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kada Ku Sake kuce Zakuyiwa Tinubu Zagon Kasa Ko Yankan Baya, MURIC Ga Gwamnonin Arewa

A wani labarin kuma fitacciyar ƙungiyar nan mai fafutukar kare hakkin Musulunci da Musulmai MURIC ta gargaɗi gwamnonin arewa kan zaɓen 2023.

NURIC ta yi kira ga wasu gwamnonin arewacin Najeriya da ake ƙishin-ƙishin suna shirin yi wa Bola Tinubu zagon ƙasa da su canza tunani kana su dakatar da shirinsu.

Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, yace bai kamata gwamnonin su yi haka ba domin babu wanda ya cancanta da zama shugaban ƙasa fiye da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel