Hamza Al-Mustapha Ya Bayyana Manyan Matsalolin da Za a Fuskanta a Zaben 2023

Hamza Al-Mustapha Ya Bayyana Manyan Matsalolin da Za a Fuskanta a Zaben 2023

  • Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi bayani mai ban tsoro a yayin da ake shirin gudanar da zaben 2023
  • Tsohon sojan yace bayanai sun nuna makamai da kwayoyi da-dama suna barkowa ta iyakokin Najeriya
  • Al-Mustapha yake cewa wasu suna sace arzikin Najeriya, ana fakewa da ‘yan bindigan da ke kasar nan

Abuja - Hamza Al-Mustapha wanda ya yi aiki a matsayin dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, ya yi ikirarin ana shigo Najeriya da makamai da kwayoyi.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi wannan bayani a lokacin da Platinum Post ta zanta da shi a wajen wani taro a Abuja. Labarin nan ya fito a jaridar The Cable.

‘Dan takaran shugaba kasar ya tattauna a kan abubuwan da suka shafi rashin tsaro da tasirin kalubalen a zaben da za a shirya a farkon shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Inda aka Samu Cikas, Maganar Taron Dangi da Peter Obi Ta Wargaje

Tsohon sojan yake cewa jami’an tsaro sun san abubuwan da ake faruwa, inda ya jero wasu tambayoyi masu ban tsoro da ya kamata ayi nazari sosai a kansu.

Maganar Manjo Hamza Al-Mustapha

"A halin yanzu, duka hukumomin Najeriya, kuma ina fatan wakilin Shugaban ‘yan sandan Najeriya yana da labarin abin da zan tattauna a kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano cewa kwayoyi da makamai masu matukar yawa suna shigowa Najeriya ta iyakokinta.
Manjo Hamza Al-Mustapha
Hamza Al-Mustapha da Nyesom Wike Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Abin tambayar ita ce wa ake shigowa wadannan makamai? Meyasa abin ya karu? Su wanene masu sayen makaman? Wanene masu aiko da su?
Shin ‘yan siyasa ne? Mecece manufar? Ko za a iya shirya zabe? An fara samun matsala tsakanin ‘yan takara, jam’iyyun siyasa da magoya baya ne?”
Abin tambayar ita ce, wanene ke aiko da makaman nan? Za a karfafa ‘yan ta’adda masu tada zaune-tsaye ne ko kuwa harkar dabar siyasa ce?

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

- Manjo Hamza Al-Mustapha

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar Action Alliance (AA) ya kuma ce wasu miyagu suna sace arzikin kasa, suna labewa da sunan ‘yan bindiga.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya halarci wannan taro da aka yi a garin Abuja, shi ma ya bada gudumuwarsa.

Alhaji Usman Bala Mohammed ya wakici Mai girma gwamna a wajen wannan zama.

Peter Obi zai ci zabe?

An samu labari an gudanar da wani bincike a kan zaben 2023, an yi hira da mutane 2000, a karshe aka fahimci 'Dan takaran LP, Peter Obi ne ya fi farin jini.

Hasashen ya nuna ba a maganar Rabiu Musa Kwankwaso da jam’iyyarsa ta NNPP, a yankunan Kudu maso gabas da Kudu maso Kudu, LP ce take da rinjaye.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng