Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Badakalar Kwangilar Yankan Ciyawa N544m Kan Tsohon SGF Babachir Lawal

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Badakalar Kwangilar Yankan Ciyawa N544m Kan Tsohon SGF Babachir Lawal

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi rashin nasara a kotu bisa karar da shigar kan tsohon SGF Babachir Lawal
  • Hukumar yaki da rashawar ta maka Lawal da wasu mutane biyar a kotun ne kan zargin badakalar N544m na kwangila
  • Amma, kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta wanke tare da sallamar tsohon SGF din da wasu mutanen biyar, tana mai cewa EFCC ta gaza gabatar da gamsassun hujja kansu

Abuja - Babban kotun tarayya a Abuja ta sallami tare da wanke tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal da wasu mutum 5 daga laifukan badakalar kwangilar Naira miliyan 544 da hukumar yaki da rashawa na EFCC ta shigar kansu.

Kotun, a ranar Juma'a ta ce hukumar yaki da rashawar ta gaza tabbatar da laifin da ake tuhumar tsohon SSG din da wadanda ake zarginsu da shi, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kudin haram: Adadin gwamnonin da suka boye tsabar kudi ya karu, inji shugaban EFCC

Babachir Lawal
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Badakalar Kwangilar Yankan Ciyawa N544m Kan Tsohon SGF Babachir Lawal. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Dalilin da yasa kotu ta wanke tsohon SGF Babachir Lawal da sauran

Da ya ke yanke hukunci kan shari'ar, Mai shari'a Charles Agbaza ya ce ba a samu wani kwakwarar hujja ba daga shaidu 11 da EFCC ta gabatar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin ya ce EFCC ba ta tabbatar da cewa Lawal mamba ne na kwamitin shugaban kasa na Arewa maso Gabas ba ko mamba na Minsterial Tenders Board da suka tantance tare da bada kwangilar.

Hakazalika, Mai shari'a Agbaza ya ce EFCC ta gaza nuna alaka tsakanin Lawan da Hukumar bada kwangiloli da ta bada takardar amincewa kafin a bada kwangilar.

Alkalin ya sallami tare da wanke wadanda ake zargin kan tuhume-tuhume 10 da ake musu saboda rashin hujjar alakanta su da laifin da ake zargin an aikata.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Kashe Zuzurutun Kudi Har N3.2bn Da Doriya Don Yiwa Jami'ar Dan Fodio Katanga

EFCC ta gurfanar da Babachir Lawal, tare da kaninsa Hamidu Lawal; Suleiman Abubakar; Apeh Monday da kamfanoni biyu, Rholavision Engineering Limited da Josmon Technologies Limited.

An tuhume su da aikata laifuka 10 masu alaka da zamba, kan yanke ciyayi kan kudi N544m, inda suka ce ba su aikata laifin ba.

A ranar 30 ga watan Nuwamban 2020, EFCC ta sake gurfanar da Lawal a gaban Mai shari'a Agbaza.

Sauya Fasalin Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Da ke Kan Mulki, Shugaban EFCC

An sanyawa gwamnoni uku da ke kan kan mulki ido kan yadda za su yi da makuden biliyoyin da suka boye kuma suke don biyan albashin ma’aikata da su, shugaban Hukumar yaki da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya sanar da Daily Trust a zantawar da suka yi ta musamman a ranar Alhamis.

Yace samamen da suke kaiwa ‘yan canji zasu cigaba inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayansu domin amfanin kowa.

Kara karanta wannan

An Gurfanar da Mutum 16 ‘Yan Kasar Waje a Kotun Najeriya Saboda Zargin Satar Mai

Asali: Legit.ng

Online view pixel