Bidiyon Doguwar Amarya Sanye da Takalma Masu Tsini Ya Ja Hankali, Mutane Sun Hau Saman Rufi Don Kallo
- Wata kyakkyawar amarya mai da tsawo ta haddasa cece-kuce a dandalin TikTok bayan ta sanya dogon takalmi mai tsini
- A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano amaryar tana tafiyar kasaita yayin da jama’a suka kewayeta
- Kyawun da matashiyar tayi a ranar bikin aurenta ya burge masu amfani da soshiyal midiya da dama
Wani dan gajeren bidiyo da wata matashiya mai suna @queenlatifa718 ta wallafa ya nuno yadda wata doguwar amarya cikin shiga ta kece raini ta burge jama’a da irin tafiyarta ta kasaita.
Yayin da amaryar ta shiga tsakiyar taron kamar wata sarauniya, sai aka jiyo mai gabatar da taron wato MC tana kodata tare da yi mata kirari.
Doguwar amarya sanye da takalma masu tsini
Hannaye da kafafuwanta sun sha lalle lamarin da yasa mutane ke tunanin ko ta sanya babaken safar kafa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanye da takalmanta masu tsini, matashiyar ta fito tamkar wata sarauniya. Tsawonta ya sanya yawancin mutanen da ke wajen sun zama gajejjeru. Ta kuma sha rawanta cikin farin ciki.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
Firstlady ya ce:
“Ku manya da safar! Amaryar ta cika komai ya ji, sura fushka Haba tana da kyau sosai.”
cynthiadennis10 ta ce:
“Tana da kyau.”
Queen_Sheedat ta ce:
“Lalle ne fa mutane ba safa ba…habba.”
Edo ya ce:
“A ture batun wata matashiyar nan da na matukar kyau.”
Noussy_noor ta ce:
“Kalli yadda amaryar ke da tsawo, safar ce ta ja hankalina.”
Bossbaby ta ce:
“Tana da tsawo kuma da takalma masu tsini kalli tafiyarta.”
naaodeheokailey ta ce:
“Wato dole ne sai an sanya takalmi saboda dama dai da tsawonta.”
Budurwar Direban Tasi Tayi Watsi Dabai Bayan Shekaru 3 Ana Soyayya, Ta Aure Wani Kwanaki 4 Bayan Ya Kai Ta Tasha
userBilkiss ta ce:
“Wannan nice a ranar aurena, tsawon kadai.”
seyifrosh7 ta ce:
“Wato babu wanda ke magana game da mutanen da ke saman rufin.”
Odo ta ce:
“Kalle mu, mu masu tsawo muna son sanya takalma masu tsini.”
Ango ya goyo amaryarsa a kan babur zuwa wajen liyafar bikinsu
A wani labarin, wani ango ya ja hankali mutane sosai a shafukan soshiyal midiya bayan ya gudanar da shagalin bikinsa a saukake kuma iya karfinsa.
Angon dai ya yi amfani da babur dinsa wajen goyo amaryarsa zuwa wajen liyafar bikinsu kuma sun kasance cikin farin ciki sosai.
Asali: Legit.ng