Direban Tasi Ya Dinga Razgar Kuka da Hawaye Bayan Budurwarsa ta Shekara 2 Tayi Aure

Direban Tasi Ya Dinga Razgar Kuka da Hawaye Bayan Budurwarsa ta Shekara 2 Tayi Aure

  • Wata budurwa a yanar gizo ta bayar da labarin yadda budurwar direba tayi watsi da shi tare da yin wuff da wani saurayin
  • Budurwar ta bayyana cewa, an yi auren bayan kwanaki kadan da direban ya kai budurwarsa tasha kan cewa zata yi tafiya
  • Mutane da yawa da suka yi martani kan labarin cin amanar sun ce ta yuwu budurwar ta hango wani hamshaki ne don haka ta aure shi

Wata wallafar shafin Twitter da @cassy_collins_ ta bayyana yadda wani direban tasi ya shiga tashin hankali sakamakon budurwarsa da ya kwashe shekaru uku yana soyayya da ita ta auri wani ta bar shi.

Direban Tasi
Direban Tasi Ya Dinga Razgar Kuka da Hawaye Bayan Budurwarsa ta Shekara 2 Tayi Aure. Hoto daga iStock Images
Asali: UGC

A wallafar da tayi ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamban 2022, tace mutumin da ta shiga tasin shi ta tarar da shi yana razgar kuka da hawaye.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Ɓarna A Babban Kasuwa A Najeriya

Budurwar matashi tayi auren sirri

Kamar yadda tace, direban ya gane cewa budurwar da ya kai tashar mota a ranar 1 ga Nuwamban 2022 ce tayi aure bayan kwanaki hudu. Sun kuma kwashe shekaru uku suna kwasar soyayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kara da cewa:

“Ya kamata ku daina tarwatsa rayuwar mutane irin haka. Akwai mugunta gaskiya.”

Kalla wallafar a Twitter:

Jama’a sun yi martani

A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya hada sama da jinjina 20,000 tare da sake wallafa 500.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a.

@TooshModels yace:

“Ta samu wanda ya shirya. Shiri yana nufin kudi. Direban tasin bai shirya ba, nema yake yi har yanzu. Mata basu damu ba.”

@Flotus_wendy tace:

“Abu daya da nake alfahari da shi shine, ko nawa za a bani ba zan taba yi wa wani haka ba. Doka ta ce.”

Kara karanta wannan

Waye Mahaifin ki a Najeriya? ‘Yar TikTok Mai Shekaru 17 ta Siya Motar N20m

@Judriez tace:

“Wadannan labaran dama suna faruwa da gaske? Ta yaya ba za ka san cewa wanda kuke soyayya yana shirin aure ba? Hakan yana nufin ba ku da wannan kusancin kenan.”

@_greatdre yace:

“Ina tausayin matar da zai yi soyayya da ita nan gaba.”

Ba wannan bane karo na farko da mata ke yi watsi da samarinsu na tsawon shekaru tare da aure wasu saboda wasu dalilai.

Matan sau da yawa su kan yi dogaro da dalilin cewa mazan basu shirya aure ba ko kuma sun samu masu kumbar susa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel