Sauya Fasalin Naira: Dalla Zai Iya Faduwa Zuwa N200, Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Sauya Fasalin Naira: Dalla Zai Iya Faduwa Zuwa N200, Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

  • Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC) ya ce akwai yiwuwar dalla za ta fadi zuwa N200 saboda sauyin fasalin naira
  • Bawa ya ce dalilin maganar sauyin dalla ta fadi daga N880 zuwa kusan N680 cikin yan kwanaki yana mai cewa yana goyon bayan matakin na sauya fasalin naira
  • Shugaban na EFCC ya kuma yi kira ga yan Najeriya su kai rahoton duk wanda suka sani yana boye naira da ake zargin na haram ne, za ba shi kyautar kashi 5 cikin 100 na kudin idan aka gano

Shugaban hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce duba da sauya fasalin naira da za a yi, dalla na iya faduwa zuwa N200 ga duk naira 1, rahoton Daily Trust.

Bawa ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da Deutsche Welle (DW) Hausa, yana mai cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi daidai da ya amince da sauya fasalin nairan.

Kara karanta wannan

Magana ta dawo baya: Ba Mu Yanke Ranar Dawo da Jirgin Kaduna-Abuja ba – NRC

Shugaban EFCC Bawa
Sauya Fasalin Naira: Dalla Zai Iya Faduwa Zuwa N200, Shugaban EFCC, Bawa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalla za ta iya faduwa zuwa N200 - Abdulrasheed Bawa

Ya ce:

"Doka ta ce a rika sauya fasalin nairan duk shekara takwas amma mun yi shekaru 20 ba tare da yin sauyin ba.
"Hakan yasa kashi 85 cikin 1000 da kudaden da ke yawo ba a bankuna suke ba. Da wannan batun sauya fasalin ya taso, dalla ta kai N880 kuma daga baya ya sakko zuwa kimanin N680.
"Toh, ka gani idan anyi wannan sauyin dalla na iya faduwa sosai, wa ya sani watakila har zuwa N200."

Babu siyasa a cikin batun sauya nairan - Bawa

Shugaban na EFCC kuma ya ce babu siyasa a batun sauya nairan yana mai kira ga yan Najeriya su kai rahoton duk wani da boye kudin haram, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Idan ya gaji Buhari: Kwankwaso ya magantu kan ko zai ke tafiya kasar waje neman magani

Ya kara da cewa:

"Babu siyasa a cikin lamarin. Wasu sun karkatar da kudaden mutane sun boye shi yasa muke son su fito da shi kuma babu wanda ya ce kada su kawo su, abin da gwamnati ke cewa shine su ajiye kudaden a bankuna.
"Muna bawa yan Najeriya tabbacin cewa a shirye muke mu karbi duk wani rahoto kan wadanda ake zargin sun boye kudu, idan an bincika, za mu bawa wanda ya tona asirin kashi 5 cikin 100 na kudin."

Ina Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Dari Bisa Dari, Shugaba Buhari

Tunda farko, kun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewa yana goyon bayan babban bankin Najeriya CBN wajen sauya fasalin Naira dari bisa dari.

A cewar Shugaba Buhari, Najeriya za ta amfana matuka da wannan shawara da bankin ya yanke.

Ya kara da cewa bai tunanin watanni uku da aka baiwa mutane su canza kudin ya yi kadan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: An Gano Wata Babbar Mota Cike Da Kudi Yan N1000 Daga Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel