Ina Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Dari Bisa Dari, Shugaba Buhari

Ina Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Dari Bisa Dari, Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana goyon bayan babban bankin Najeriya CBN wajen sauya fasalin Naira dari bisa dari.

A cewar shugaban kasa, Najeriya za ta amfana matuka da wannan shawara da bankin ya yanke.

Ya kara da cewa bai tunanin watanni uku da aka baiwa mutane su canza kudin ya yi kadan.

Yace:

"Masu kudin haram da suka birne cikin kasa suke tsoro amma ma'aikata, yan kasuwa masu kudin hala ba zasu fuskanci wani matsala ba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya bayyana hakan a hirar da yayi yan jaridar Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Kawo Dalilin Goyon Bayan CBN Kan Buga Sabon Kudi

Za'a haska wannan hira ranar Laraba a tashar Tambari TV.

Yace:

"Shugaba Buhari a ranar Lahadi ya bayyana cewa shirin da babban bankin Najeriya CBN yayi na fitar sabon samfurin Naira na bisa goyon baya na kuma kasar nan za ta amfana da hakan."
"A hira da gabatar da harshen Hausa tare da shahrarren dan jarida Halilu Ahmed Getso, da Kamaluddeen Sani Shawai kuma za'a haska da safiyar Laraba a Tambari TV Nilesat, Shugaba Buhari ya bayyana jawabin da CBN yayi masa don gamsar da shi tattalin arzikin Najeriya zata amfana ta da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel