Kar a Kira Ni Bayan Karfe 7 Na Dare, Sabon Ango Ya Gargadi Jama’a a Wani Bidiyo
- Wani dan Najeriya da ya angwance ya sa jama'a dariya a wurin bikinsa yayin da ya gargadi abokansa da cewa kada su sake kiransa bayan karfe 7 na dare
- A wani bidiyon da aka yada a kafar TikTok ta hannun Lumigold Alaga, angon mai suna Mr Akin ya yi maganarsa da nuna da gaske yake
- Bidiyon ya shahara a TikTok da sauran kafofin sada zumunta, lamarin da ya jawo cece-kuce da dama daga jama'a
Bidiyon da aka yada na wani sabon ango ya ba da mamaki yayin da yake gargadin abokansa da ke kiransa a waya bayan karfe 7 na dare.
Mutumin mai suna Mr Akin ya yi gargadi ga jama'a, a wani jawabi da ya yi na godiya ga wadanda suka halarci bikinsa.
Da yake tare da amaryarsa a hannun hagunsa, Mr Akin ya bayyana gargadinsa cikin barkwanci.
Wannan sanarwa ta gargadi dai ta jawo jama'a sun tuntsure da dariya, har da amaryar kowa ya yi dariya da jin batunsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon da Lumigold Alaga ya yada a TikTok ya jawo cece-kucen jama'ar intanet.
Ya zuwa yanzu, an ga dangwale 15,000, martano 138 akalla kuma mutane 172 ne suka yada bidiyon a TikTok.
Martanin jama'a
Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:
@Golden Touch salon yace:
"Baba yana amfani da salo ne wajen ankarar da 'yan matansa na gefe."
@Medical Approach yace:
"A matsayina na likita, idan na fadi haka, babban likita ne zai tsaya yana jira ne sa safe saboda ba da bahasi."
@Ashantybabe19 yace:
"Na taya ka murna dan uwa, yau ne wannan rayuwar gauranta ke kara bata min rai."
@Temmy Precious317 yace:
"Dariya kawai nake ta yi mai wawa."
@Fordculture yace:
"Ina son suturar da matar ta sanya, yana da matukar kyau."
@rukayaalaba yace:
"Ina taya ku murna"Allah madaukaki ya albarkaci gidanku."
@ATB yace:
"Allah Allah nake nayi aure."
@ItsSinmi yace:
"Kun dai ji ko? Ya ce 7 na dare fa! Ta yi kyau sosai."
An kirkir takalmin gayu mai ban mamaki
Yayin da duniyar gayu ke kara ta'azzara, wani ya kirkiri takalmi ban mamaki, an yi shi sak siffar kafar dan adam.
Mutane da dama a kafar sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan takalmi mai dauke da kaho da dunduniya mai tsawo.
Asali: Legit.ng