RMAFC ta jero Shugabannin Hukumomin da Albashinsu Ya Fi Na Shugaban kasa tsoka

RMAFC ta jero Shugabannin Hukumomin da Albashinsu Ya Fi Na Shugaban kasa tsoka

  • Shugaban Hukumar RMAFC ya tsaya tsayin-daka a kan cewa sai an yi wa wasu jami’ai karin albashi
  • Mohammed Shehu yace sun dauki matakin ne saboda akwai ma’aikatan da sun fi shugaban kasa albashi
  • RMFAC tace albashin shugabannin irinsu NPA, NCC da Gwamnan CBN ya zarce na Muhammadu Buhari

Abuja - Hukumar RMAFC mai alhakin yanke albashin ma’aikata da ‘yan siyasa a Najeriya, ta dage a kan batun yin karin albashin ga ‘yan siyasa.

This Day tace shugaban RMAFC na kasa, Mohammed Shehu ya kare matakin nan da suka dauka, yace bai dace wani ya fi shugaban kasa albashi ba.

Shehu ya ambaci hukumomi da cibiyoyin gwamnati irinsu NCC mai kula da harkar sadarwa da babban bankin CBN a cikin masu albashi mai tsoka.

Haka zalika Shehu yace jami’an hukumar NPA mai kula da tashohin ruwa, su na tashi da kudin da ya zarce samun Mai girma shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Akwai 'yan mowa da 'yan bora

An rahoto Shehu yana cewa hukumomin da ke tatsowa gwamnatin Najeriya kudin shiga, sun fi sauran takwarorinsu albashi saboda a hana su sata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka zanta da shi a wani shiri a gidan talabijin na Channels, shugaban na RMFAC ya bayyana cewa akwai matsala a game da tsarin albashin kasar.

RMFAC
Rantsar da Shugaban RMFAC Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shehu yace hukumar da yake jagorantar ta na duba tsarin albashin ma’aikatan kamfanin mai na kasa na NNPC, FIRS mai tara haraji da wasu hukumomin.

Wasu sun fi shugaban kasa albashi

“Mutanen Najeriya da-dama ba su san akwai bambanci ba. Meyasa shugaban wata hukuma zai rika karbar albashin da ya fi na shugaban kasar Najeriya?
Amma haka abin yake. Akwai NCC, NPA da Gwamnan CBN. Kun san kudin da Gwamnan CBN yake tashi da shi, ya zarce na shugaban tarayyar Najeriya?

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta dura Jigawa, ta kama wani babban na hannun daman gwamna

- Mohammed Shehu

A ra’ayinsa, bai kamata a samu wani jami’in gwamnati ko ma’aikacin da albashin da yake karba, ya fi karfin abin da ake biyan Mai girma shugaban kasa ba.

A hirar da aka yi da shugaban na Hukumar RMAFC, ya nuna cewa za a taba albashin ma’aikata ne da nufin a samu daidaito, ba ayi masu karin kudi kurum ba.

Fetur ya kara tsada

An samu labari kungiyar ‘Yan kasuwan Najeriya ta ce man fetur ya yi tsada, don haka babu maganar gidajen mai su saida litarsu a kan N185 a yanzu.

Idan aka yi la’akari da hauhawar farashi a kasuwa, halin tsadar rayuwa da tashin Dala, zai yi wahala litar man fetur bai zarce N200 a gidajen mai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng