labarai da suka yi fice daga jaridun Najeriya a yau Litinin

labarai da suka yi fice daga jaridun Najeriya a yau Litinin

Manyan labarai da sukayi fice daga jaridun Najeriya a yau litinin 1 ga watan Augusta

labarai da suka yi fice daga jaridun Najeriya a yau Litinin

Jaridar daily trust ta ruwaito cewa, sarkin musulmai sultan na sokoto, alhaji abubakar sa’ad yayi kira ga aure a tsakanin musulmai da kirista domin kawo zaman lafiya da ci gaba a kasar. Bisa ga jaridar Punch, hukumar zabe na jihar Adamawa, ta bayana sakamakon zaben da akayi a karamar hukumomi na jihar a ranar Asabar.

Shugaban hukumar, Alhaji Isa Shettima ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce ta lashe zaben chiyaman a karamar hukumomi 18 da aka fada sakamakonsu, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a garin Yola. Ya kuma ce an soke zaben karamar hukumar Michika, Lamurde da Numan, an kuma bayyana 6 ga watan Augusta a matsayin ranar da za’a sake zaben.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya maida martani kan kwace mulkin Buhari

A cewar jaridar The Nation, wata babban kotun tarayya dake Abuja tayi kira ga darakta, na shashin dake biye da doka na kwasatam din Najeriya, da kuma wani Lauya a sashin,S.I. Bello kan mutuwar wani da ake zargi, Abubakar Rilwan.

Mai shari’a Nnamdi Dimgba, wanda ke wakiltan maishari’an kotun, ya bukaci daraktan dake bye da doka da Bello da su garfana a gaban kotu a ranar 4 ga watan Augusta domin suyi bayani kan dalilin da zaisa kada su fuskanci shari’a kan kin bin umarnin kotu na cewa su tabbatar Rilwan ya samu kulawar likita.

Daga karshe jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Abdulmumin Jibrin, tsohon shugaban majalisa ya bayyana cewa majalisar wakilai wanda shi ya kasance mamba a cikinta yace dukkansu masu cin hanci da rashawa ne.

Ya kuma zargi kakakin majalisar, Yakubu Dogara, mataimakinsa, Yusuf Lasun,  Alhassan Doguwa da kuma ahugaban tsirarun yan majalisa, Leo Ogor, da yin sama da fadi kan kasafin kudin naira milliyan 40.

Asali: Legit.ng

Online view pixel