An Sako ’Ya’yan Tsohon Akanta Janar Na Zamfara Bayan Watanni 7 a Hannun ’Yan Bindiga
- ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ‘yan mata biyar ‘ya’yan tsohon akanta-janar na jihar Zamfara
- Bayan shafe watanni, ‘yan bindiga sun nuna bidiyon yadda suka ba ‘yan matan bindiga tare da cewa za su mai dasu ‘yan ta’adda
- A yau muka samu labarin an sako su, yanzu haka suna hannun gwamnati ana kula da lafiyarsu
Jihar Zamfara - ‘Yan bindiga sun saki ‘ya’ya mata biyar na Abubakar Furfuri, tsohon akanta-janar na jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya da suka sace.
An ruwaito cewa, an sace ‘yan matan biyar ne a gidansu da ke Furfuri, wani yanki a karamar hukumar Bungudu ta jihar a watan Maris din ta gabata.
Zailani Bappa, mai ba gwamnan Zamfara Bello Matawalle shawari kan harkokin wayar da kan jama’a ne ya tabbatar da an sako ‘yan matan.
Ya ce an mika su ga gwamna Matawalle a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda aka ceto ‘yan matan
A cewar Bappa, hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda ne ya kai ga ceto wadannan ‘yan mata ba tare da wata cutarwa ba.
Sai dai, Radio Nigeria ta ce ta tattauna da mahaifin 'yan matan ta wayar tarho, inda ya ce ya ba 'yan bindigan makudan kudade kafin sako 'ya'yan nasa.
Gwamna Matawalle ya yaba wa hukumonin tsaro bisa wannan kokari, ya kuma bukace su da su kara kokari wajen dakile ‘yan bindiga a jihar.
Ya kuma bayyana cewa, rahotannin sirri sun nuna an sace ‘yan matan ne bayan da ‘yan bindigan suka samu bayanan sirri daga wasu na kusa da ahalin tsohon akantan.
Daga nan ya bukaci ‘yan jihar da su dage wajen yakar masu kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.
Ya ce:
“Ba don masu kai bayanan sirri ba, da tuni cikin karfin iko an gama da ‘yan bindiga cikin sauki.”
Daga karshe ya umarci jami’ai da su kai ‘yan matan a yi musu gwajin lafiya na musamman tare da hada su da iyalansu daga baya.
A watan Oktoba, wani bidiyo ya yadu na yadda ‘yan bindigan suka ba ‘yan matan makamai tare da barazanar mai she su ‘yan bindiga idan ba a biya su kudin fansa ba.
Asali: Legit.ng