Yanzu-yanzu: Rayuka 5 sun hallaka a rikicin Irigwe da Fulani a jihar Plateau
Akalla rayuka biyar sun salwanta a wani sabuwar rikici da ramuwar gayya tsakanin matasan Irigwe da Fulani a karamar hukumar Bassa da ke jihar Flato.
Majiyoyi a garin Bassa ya bayyana cewa mazauna garin sun ga gawan matasan Irigwe uku wadanda ake zargin Fulani Makiyaya suka kashe.
A gefe daya kuma, shugaban kungiyar Miyetti Allah, Danladi Ciroma, ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa an hallaka Fulani Makiyaya biyu masu suna Musa Idris da Anas Zakariya, a Kamarun Chawai ranan Talata kuma ana zargin matasa Irigwe da wannan aika-aika.
Ya bayyana wannan sabon kashe-kashen a matsayin siyasa kawai, inda yace “Wannan gwamnati da jami’an tsaron na iyakan kokarinsu amma kada wadannan matasa su yarda yan siyasa su yaudare su.”
Wani majiyan jami’an tsaro ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa ramuwar gayya ce. Matasan kabilun guda biyu ke tayar da rikici.
Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Manjo Adam Umar ya tabbatar da wannan kashe-kashen inda yace suna gudanar da bincike cikin al’amarin.
KU KARANTA: Ku daina kulle gidajen man fetur – NUPENG ya gargadi DPR
Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Tyopev Terna, yace kwamishanan jihar Adie Undie ya gana da mazauna Bassa, Jos, Riyom, Barikin Ladi da makiyaya kuma ya gargadesu akan fadace-fadace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng