Kahinde Na Aura, Ba Tagwaye Biyu Ba, Inji Muslmin da Aka Ce Ya Auri 'Yan Biyu a Rana Daya

Kahinde Na Aura, Ba Tagwaye Biyu Ba, Inji Muslmin da Aka Ce Ya Auri 'Yan Biyu a Rana Daya

  • Lukman Musa Bamidele, wani matashi dan garin Ede a jihar Osun da aka ce ya auri 'yan mata biyu tagwaye a rana daya ya yi magana a wani bidiyo
  • A wani bidiyon da aka yada, Bamidele ya karyata rahotannin da ke cewa ya auri 'yan tagwaye, ya kuma bayyana gaskiyar abin da ya faru
  • A cewar angon, kawai tagwayen sun saba sanya sutura iri daya ne, don haka suka saka a ranar bikinsa da daya daga cikinsu

Ede, jihar Osun - Matashi dan Najeriya mai suna Lukman Musa Bamidele da aka yada ya auri mata biyu tagwaye a rana daya a yankin Ede na jihar Osun ya karyata jita-jitan da ake yadawa.

A wani idiyon da aka yada a kafar sada zumunta, matashin ya bayyana cewa, ya auri daya daga cikin tagwayen ne mai suna Kahinde sabanin abin da wasu jaridu suka yada.

Kara karanta wannan

Kebera yake sha? Bidiyon mataccen takalmin da wani ya saka ya je neman aure ya ba mamaki

Lukman dai ya bayyanawa jama'a cewa, tagwayen sun saba sanya sutura kala daya, don haka ne ma suka yi irin hakan a bikinsa da daya daga cikinsu.

Daga nan ne ya yi kira ga 'yan Najeriya da suka daina yada labaran karya, inda ya kara cewa, kawai dai shakuwa ce irin ta tagwaye wannan yasa aka ga sun yi shiga iri daya.

Matashin da aka ce ya auri 'yan biyu ya magantu
Kahinde Na Aura, Ba Tagwaye Biyu Ba, Inji Muslmin da Aka Ce Ya Auri 'Yan Biyu a Rana Daya | Hoto: Ayekooto
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana wannan batu ne a bidiyon da aka yada a Twitter a hannun @DeeOneAyekooto.

Musulmi ya auri mata biyu a rana daya

Idan baku manta ba, a baya rahotanni sun karade kasa kan yadda wani matashi ya auri mata biyu tagwaye a rana daya.

Kuma an ruwaito cewa, musulmi ne yayin da aka yada wnai bidiyi da ke nuna lokacin da matashin ke zaune a wurin aure.

Kara karanta wannan

Arewa ko Kudu? Peter Obi ya fadi yankin da zai mayar da hankalinsa a kai idan ya gaji Buhari

Wani dan jarida, Obarayese Sikiru ne ya yada labarin a Twitter, inda yace:

"Mutum ya auri yan biyu ranar Asabar a Ede, jihar Osun."

Budurwa Ta Yada Bidiyon Kalan Takalmin da Saurayinta Yazo Dashi Neman Aurenta

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya mai suna @black.teenah ta yada bidiyo mai ban dariya na wani manemin aurenta.

Kamar yadda ya bayyana, mutumin ya zo gidan su budurwar ne domin neman aurenta.

Yayin da ya cire takalminsa ya shiga gidan su Teenah, ta kadu bayan ganin irin takalmin da ya zo dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel