Gwamna Sanwo-Olu Ya Burge Mutane Da Dama Yayin da Ya Karanto Suratul Fatiha, Bidiyon Ya Yadu

Gwamna Sanwo-Olu Ya Burge Mutane Da Dama Yayin da Ya Karanto Suratul Fatiha, Bidiyon Ya Yadu

  • Duk da kasancewarsa Kirista, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas ya nuna cewa ya iya karatun Al-Qur’ani yayin da ya karanto Fatiha tsaf
  • An gano gwamnan a cikin wani bidiyo da ya yadu yana karanto shafin farko na Al-Qur’ani mai girma tare da mataimakinsa, Obafemi Hamzat da kakakin majalisar jihar, Obasa
  • Bidiyon ya haifar da martani daga yan Najeriya, wanda ke ganin hakan ya tabbatar da cewar yankin kudu maso yamma na da saukin kai a bangaren addini

LagosA Najeriya, ana kallon yankin Yarbawa wato kudu maso yamma a matsayin yankin da yafi ko’ina juriya a bangaren addini. Sai ka ga a dangi guda akwai Musulmai kuma akwai Kirista.

Saboda haka, Musulmai da kiristoci a yankin sun san addinin junansu ciki da bai.

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023

Gwamnan Lagas a taro
Gwamna Sanwo-Olu Ya Burge Mutane Da Dama Yayin da Ya Karanto Suratul Fatiha, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Ayekooto
Asali: Facebook

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas wanda ya kasance kirista, ya kara da tabbatar da hakan bayan an gano shi a cikin wani bidiyo da ya yadu yana karanto suratul Fatiha da ka.

A wani bidiyo da shafin Ayekooto, @DeeOneAyekooto, ya wallafa a Twitter, Gwamna Sanwo-Olu ya karantu shafin farko na Al-Qur’ani mai girma tare da mataimakinsa, Obafemi Hamzat da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Lagas, Mudashiru Obasa, wadanda su din Musulmai ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A kudu maso yamma, Musulmi na hakika zai iya karanto Psalm 23 sannan dole Kiristan kwarai ya iya karanta Fatiha.
“Misali da Sanwo-Olu!” Ayekooto ya wallafa tare da bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani

ade dstv, @adedstv, ya ce:

“Kwarai da gaske!!! Ina karanta FATIHA ,INA ATAENA, QULIHU ALLAHU ba tare da gargada ba! Amma kuma, babu Musulmi ko daya a dangina.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

“Mun koya ne daga makaranta da unguwarmu! Zan iya kiran sallah a sawwake. Dalili, saboda akwai masallaci a gidan da ke kusa dani! Addini ba yaki bane a nan!”

Tajudeen Raji, @TajudeenR, ya ce:

“Hakan take a nan fa. Zan iya karanta addu’ar Musulmai da na kirista a baccina. Kuma ni dan hakika ne idan aka zo kan addini.”
“Mu rayu cikin aminci. Soyayya daya.”

IGBOMINA, @Optimistic_Ade, ya ce:

“Wannan ya yi nisa ma. Ni da nake da kanne kiristoci biyu da kanne Musulmai biyu. Addini ba zai iya rabamu ba.”

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce addu'a Najeriya ke bukata daga gwamnatin Amurka maimakon gargaji wanda ya jefa mutane cikin rudani.

Ministan ya bayyana cewa gargadin da Amurka tayi kan yuwuwar kai harin ta'addanci a Abuja ya jefa jama'a cikin tsoro sannan ya razanar da yan Najeriya ta yadda har sun gaza daukar matakin da ya dace, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Jerin Duka Abubuwa 20 da Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Zai Yi Idan Aka Zabe Shi a NNPP

Magashi ya yi magana ne yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatar tsaro na 2023 a gaban kwamitin majalisar wakilai, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng