Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Kwamishinan Ayyuka Na Nasarawa A Gidan Gyaran Hali

Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Kwamishinan Ayyuka Na Nasarawa A Gidan Gyaran Hali

  • Wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Nasarawa ta bada umurnin tsare Kwamishinan ayyuka na jihar, Idris Mohammed
  • An gurfanar da Mohammed da wasu mutane biyar a kotun ne kan zarginsu da katare wani fili da tsorata mai filin
  • Alkaliyar kotun ta bada umurnin a tsare kwamishinan da gidan gyaran hali ne saboda cigaba da saba umurnin kotu da ya ke yi

Nasarawa - Babban kotun majistare da ke zamanta a Uke, karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ta bada umurnin tsare Injiniya Idris Mohammed saboda rashin gurfana a kotu a ranar Litinin, Daily Trust ta rahoto.

An gurfanar da Mohammed, wanda shine kwamishinan ayyuka da raya karkara a jihar, a kotu ne kan zargin hadin baki don aikata laifi, ketare fili da makirci da wani Injiya Idris Aliyu-Bori da wani suka shigar.

Kara karanta wannan

An samu tsaiko: Kotu ta rushe zaben fidda gwanin sanatan APC a jihar Arewa

Nasarawa map
Ketare Kasa: Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Kwamishinan Ayyuka Na Nasarawa A Gidan Yari. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

An zargin Mohammed da wasu mutane biyar da wasu mutane biyar da laifin ketare wani fili na wanda ya yi karar da kuma makirci bayan tsoratar da wanda ya shigar da karar.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Barista N.E. Emmanuel, ta bukaci a kwace belin da aka bawa kwamishinan a baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewa kotu ta gayyaci wanda ya karbe shi beli don ya zo ya bada dalilin da yasa ba zai rasa kudin belin da ya bada ba na karbar belin.

Amma, lauyan wanda aka gurfanar, Barista G.O. Idu, bai amince da shawarar kamawar ba.

Hukuncin alkaliyar kotun

Alkaliyar kotun, Aisha Abdullahi, a hukuncinta, ta jadada bukatar lauyan mai karar kuma ta bada umurnin nan take a kamo kwamishinan, tana mai cewa dalilin hakan shine cigaba da kin bin umurnin kotu.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Majalisa ta gano ba a aikin wutar Mambila, tuni EFCC ta fara bincike

Alkaliyar ta kara da cewa a cigaba da tsare Idris a gidan gyaran hali na Keffi.

Sannan aka dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Nuwamban 2022.

Kotu Ta Tura Farfesan Da Ta Yi Wa 'Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' Gidan Yari

Wata kotun majistare da ke zamanta a birnin taraa Abuja, ta bada umurnin a tsare Farfesa Zainab Duke Abiola a gidan yarin Suleja kan zargin cin zarafin Teju Moses, yar sanda mai tsaronta.

An gurfanar da farfesan ne tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, a ranar Juma'a 23 ga watan Satumba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel