Kotu Ta Tura Farfesan Da Ta Yi Wa 'Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' Gidan Yari

Kotu Ta Tura Farfesan Da Ta Yi Wa 'Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' Gidan Yari

  • Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Abuja ta umurci a bawa Farfesa Zainab Duke Abiola masauki a gidan yari
  • An gurfanar da Zainab ne tare da yar aikinta Rebecca Enechido kan zarginsu da cin zarafin yar sanda mai tsaron farfesan
  • Tunda farko, Zainab ta musanta zargin da ake mata na cin zarafin yar sandan tana mamakin yadda IGP na yan sanda zai keta hakkinta

Abuja - Wata kotun majistare da ke zamanta a birnin taraa Abuja, ta bada umurnin a tsare Farfesa Zainab Duke Abiola a gidan yarin Suleja kan zargin cin zarafin Teju Moses, yar sanda mai tsaronta.

An gurfanar da farfesan ne tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, a ranar Juma'a 23 ga watan Satumba, Daily Trust ta rahoto.

Farfesa Zainab
Kotu Ta Tura Farfesan Da Ta Yi Wa 'Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' Gidan Yari. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bidiyo da ya bazu a ranar Laraba, an ga yar sandan zaune a kasa tana bukatar a kai ta asibiti yayin da jini ke zuba daga jikinta.

Yan sanda sun zargi Abiola, lauya kuma mai rajin kare hakkin bil adama, ta yunkurin aikata kisa da cin zarafi da gangan da cin amana.

A kotun, a ranar Juma'a, an hana farfesan beli yayin da aka daga cigaba da shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Oktoban 2022.

Zainab ta musanta zargin cin zarafin yar sandan

Tunda farko, Farfesa Zainab ta musanta cewa ta ci zarafin yar sandan tana cewa abin mamaki ne IGP zai keta 'hakkin yar kasa mai bin doka kuma a dauki hotunanta a wallafa su a kafafen watsa labarai a karkashin gwamnatin demokradiyya.'

Cikin sanarwar da kungiyar lauyoyi na Afrika-Turai suka fitar ta ce ba ta taba cin zalin kowa ba.

Gaskiyan abin da ya faru, In ji Zainab

Zainab ta ce a ranar 20 ga watan Afrilun 2022 IGP ya tura mata dogari mai tsaronta a matsayinta na lauyar tuntuba na rundunar yan sanda amma daga bisani ta gano yar sandan na cikin wadanda suka ci zalin mutane yayin zanga-zangar Endsars.

Hakan yasa daga bisani ta ce ba za ta yi aiki da yar sandan ba ta umurci to kama hedkwata a ranr 19 ga watan Satumba amma ta dawo daren ranar da makamai da bindiga tana barazanar kashe kowa a gidan hakan ya janyo rikici.

Daga karshe ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya kori Sufetan Yan Sanda, Alkali Baba Usman, kuma ya fuskanci hukunci kan abin da ta kira cin zarafinta.

An Cafke Farfesan Da Ta Yi Wa Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' A Abuja, Yan Najeriya Sun Yi Martani

A baya, kun ji cewa yan sanda sun kama wata lauya kuma mai rajin kare hakkin bil adama a Abuja, Farfesa Zainab Duke Abiola, kan dukkan yar sanda mai tsaronta, Sufeta Teju Moses.

An kama Farfesan tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, kan cewa sun duki yar sanda mai tsaron saboda ta ki yin wasu ayyukan gida da ta saka ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel