Yanzu-Yanzu: An Kama Dan Takarar Jam'iyyar Kwankwaso da Tsabar Kudi N326m da Daloli $610,500

Yanzu-Yanzu: An Kama Dan Takarar Jam'iyyar Kwankwaso da Tsabar Kudi N326m da Daloli $610,500

  • An kama wani dan siyasa daga jihar Kogi, Ismaila Atumeyi, a Abuja kan samunsa da hannu a badakalar biliyan N1.4 sakamakon kutse da aka yiwa banki
  • EFCC ta kama Atumeyi, dan takarar kujerar dan majalisar dokokin jihar Kogi a jam’iyyar NNPP da tsabar kudi miliyan N326 da $140,500
  • An kama dan takarar da NNPP tare da wasu mutum biyu wadanda suka taimaka masa wajen yin kutsen

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama dan takarar kujerar dan majalisar dokokin jihar Kogi a karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Ismaila Atumeyi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an kama Atumeyi ne da tsabar kudi har naira miliyan 326 da kuma dala 140,500.

An kama Atumeyi wanda ke son wakiltan mazabar Ankpa 11 a majalisar dokokin jihar Kogi a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, tare da wani Joshua Dominic, wanda ake zargin madugun mai damfara ne.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Jami'an EFCC
Yanzu-Yanzu: An Kama Dan Takarar Jam'iyyar Kwankwaso da Tsabar Kudi N326m da Daloli $610,500 Hoto: vanguardngr.ng

An damke mutanen ne a wani samame da aka kai unguwar Macedonia, Queens Estate, Karsana, Gwarinpa, Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, daga cikin wadanda aka kama kan zambar harda Abdulmalik Femi, wani tsohon ma’aikacin baki, wanda ake zargin shine ya bayar da bayanan cikin gida da suka taimaka a harin da tawagar suka kaiwa bankin.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewar an kama Femi ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, a otel din Radisson Blu da ke Lagas, rahoton Daily Trust.

Ya ce:

“Bayan kamun nasa, an gudanar da bincike a gidansa da ke Morgan Estate, Ojodu inda aka samu jimlar dala $470,000.”
“An kama wadanda ake zargin ne sakamakon bincike da aka shafe watanni aka yi kan kutse da wasu tawagar yan damfara suka yiwa wasu bankuna inda suka janye kudi har naira biliyan 1.4.”

Kara karanta wannan

Dalilai 5 Dake nuna Peter Obi Ba zai Samu Nasara A Zaben 2023, Fitch Solutions

An yi zargin cewa madamfarar sun tura miliyan N887 zuwa asusun kamfanin Fav Oil and Gas limited, inda daga nan aka baiwa yan chanji daban-daban kudaden da dilallan motoci don sauya su da daloli da kuma siyan manyan motoci.

Dominic, wanda an sha kama shi kan damfara, ya taimakawa Atumeyi wajen aiwatar da kutsen ta hannun Abdulmalik.

Jami’an rundunar yan sanda ta musamman sun kama Dominic a watan Mayun 2021 kan zargin badakalar naira biliyan 2 na hannun jari. An yi zargin cewa ya damfari mutum fiye da 500 a wani shirin zuba jari.

Kadarorin da EFCC ta samu daga hannun wadanda ake zargin

An tattaro cewa EFCC ta samo manyan motocin Range Rover SUV guda biyu daga hannun mutum biyu da aka kama a Abuja.

Uwujaren ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu nan ba da jimawa ba domin an kammala bincike.

Kara karanta wannan

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

A halin da ake ciki, hukumar ta nuna damuwa game da yadda ake samun karuwar hare-haren bankuna ta yanar gizo da kuma halin bankunan na rashin son kai rahoton irin wannan lamari ga hukumomin doka.

Daga Karshe Bola Tinubu Ya Amsa Bukatar Yan Najeriya, Ya fadi Hanyoyin Arzikinsa

A wani labarin, mun ji cewa bayan yan Najeriya da dama a fadin duniya sun nemi jin ta bakinsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya magantu kan tushen arzikinsa.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin kungiyar NAPOC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa yana da gidajen gas biyu a birnin Landan, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel