Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyayensu, Ya Dauko Marayu, Zai Kashe Masu N300m
- Gwamnatin jihar Borno ta ware N300m domin marayu su samu damar da za su je makarantun boko
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci a taimakawa yaran ‘yan sa-kai da suka mutu a yakin Boko Haram
- Baya ga makaranta da za a kai ‘ya ‘yansu, Gwamnatin Zulum za ta raba masu kudi, abinci da kuma tufafi
Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada sanarwar tallafin kudin karatu ga marayun da suka rasa iyayensu a yakin Boko Haram.
Hukumar dillacin labarai ta kawo rahoto cewa Mai girma Gwamnan zai biya N300m domin ‘ya ‘yan ‘yan kato-da-gora su samu damar yin karatun zamani.
Akwai dakarun sa-kai da suka rasa rayukansu a yunkurin kare jihar Borno daga ‘Yan Boko Haram, daga ciki akwai CJTF, ‘yan kato-da-gora da ‘yan farauta.
Da Gwamnan jihar Borno yake bayani a ranar Talata a garin Maiduguri, yace ya kara albashin da ake biyan wadannan dakaru daga N20, 000 zuwa N30, 000.
Gwamna ya yi karin albashi
Baya ga karin albashin, Vanguard tace Mai girma Babagana Umara Zulum ya yi alkawarin zai shigo da tsarin bada kyautan kudi duk karshen shekara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Farfesa Babagana Zulum yace wadannan mutane da suka sa kansu a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda, sun taimaka sosai wajen kawowa jihar kwanciyar hankali.
Gwamnan yace ‘yan sa-kai sun lakanci wuraren da ake shiga, don haka sun bada gudumuwa sosai.
Za a tallafawa marayun da aka bari
Gwamnain Zulum tayi alkawarin cewa ba za tayi watsi da iyalin wadanda suka kwanta dama ba, yace ya kawo tsari domin gano inda marayunsu suke.
Bugu da kari, an ji Gwamna Zulum ya bada sanarwar raba kudi, kayan abinci da tufafi domin taimaka iyalin da wadannan Bayin Allah suka mutu suka bari.
Kafin ya gama jawabinsa a jiya, Gwamnan na Borno ya jinjinawa sojoji da sauran jami’an tsaro a kan rawar da suka taka wajen kawo zaman lafiya a Borno.
Hukumar NDDC za ta taimaka
Shugaban kwamitin tallafin, Alhaji Kaka-Shehu Lawan yace sun tantance mata 110 da maza 190 da za su amfana da wannan tsari da gwamna ya shigo da shi.
Shugaban hukumar NEDC na kasa, Mohammed Alkali wanda ya samu wakilcin Grema Mustafa, ya yaba da wannan, kuma ya bayyana irin na su tanadin.
A binciki Natasha - Kogi
Kun samu labari Kwamishinan yada labarai na Kogi, Kingsley Fanwo yana so jami’an tsaro su shirya bincike na musamman a kan Natasha Akpoti Uduaghan.
Ana tunanin Natasha Uduaghan tana da alaka da wani Safiu wanda shi ake zargin ya hallaka mutane kimanin 40 da aka kai hari kwanaki a coci a jihar Ondo.
Asali: Legit.ng