Sanusi II: Maganar Shirin Cire Ajami daga Takardun Kudin Najeriya Ba Gaskiya ba ne

Sanusi II: Maganar Shirin Cire Ajami daga Takardun Kudin Najeriya Ba Gaskiya ba ne

  • Muhammadu Sanusi II ya karyata jita-jitar da ke yawo na yunkurin cire Ajami daga kudin Naira
  • Tsohon gwamnan babban bankin CBN yace ya yi magana da Gwamna mai-ci a kan wannan batu
  • Sanusi II ya nuna Godwin Emefiele ya tabbatar masa ba za a cire rubutun Ajami daga kudin kasar ba

Lagos - Tsohon gwamnan babban bankin CBN, Muhammadu Sanusi II, ya fito ya yi magana game da jita-jitar cire rubutun Ajami daga takardun Naira.

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a shafinsa na Twitter, an ji Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana karyata rade-radin da ke yawo.

Ganin har wasu malaman addini sun fara fashin-baki a kan lamarin alhali bai tabbata ba, Sanusi II ya yi kira ga malaman su daina aiki da jita-jita.

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

"Akwai maganganu da suke ta yawo a kan canza kudin Naira, na ji malamai dabam-dabam; wasu masu zafi a kan zargin za a cire Ajami daga Naira.

Nayi magana da 'Yan CBN - Sanusi II

Ina so in yi amfani da wannan dama, in tabbatarwa al’ummar Musulmi cewa babu gaskiya a cikin wannan maganar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babu gaskiya ko kadan a zargin cire Ajami daga Naira. A lokacin da aka fara maganar, mun yi magana da mutanen CBN.
Sanusi II
Muhammadu Sanusi II Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Sun tabbatar mani da cewa babu wannan maganar. Da maganar tayi zafi, ni kai na, nayi magana da gwamnan banki
Gwamnan babban banki ya tabbatar mani da cewa babu maganar cire Ajami daga kan Naira. - Muhammadu Sanusi II

A daina aiki da jita-jita

"Don Allah malamai a daina aiki da jita-jita, mun san malaman da ke magana, suna magana ne a kan abin da aka kawo masu ba tare da bincike ba."

Kara karanta wannan

2023: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Yunkuro Wa, Sun Huro Sabuwar Wuta a Jam'iyyar PDP

- Muhammadu Sanusi II

Khalifan na Tijjaniya ya tunawa al’umma koyarwar addinin Musulunci game da yin bincike idan wani ya kawo labari, kafin a dauki mataki saboda nadama.

EFCC ta ji dadin canza Naira

A baya an ji labari Abdulrasheed Bawa ya fadawa 'Yan majalisar dattawa irin nasarorin da hukumar da yake jagoranta ta samu a shekarar nan ta 2022.

Shugaban EFCC yace sun gurfanar da ‘yan damfara kusan 3, 000. Baya ga haka, Bawa yace canza takardun kudi da Gwamnan CBN zai yi, mataki ne mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel