Yadda Gwamnan PDP Ya Rabawa Jihohi 5 Gudumuwar Naira Biliyan 2 a Shekara 1

Yadda Gwamnan PDP Ya Rabawa Jihohi 5 Gudumuwar Naira Biliyan 2 a Shekara 1

  • Abin da Nyesom Wike ya bada a matsayin kyauta ko kuma tallafi daga bara zuwa yanzu ya zarce N2bn
  • Gwamnan ya kashewa jihohin Sokoto, Kaduna da Legas Naira biliyan 2.1 a shekara da ‘yan watanni
  • Nyesom Wike ya yi rabon kudi har a Arewacin Najeriya a lokacin da musiba ta aukawa mazauna yankin

Port Harcourt, Rivers – Mai girma Gwamna Nyesom Wike mai mulkin jihar Ribas ya saba taimakawa jihohi da daidaikun mutane da-dama da tallafin kudi.

Mun fahimci a watanni 15 da suka wuce, gwamnan na Ribas ya bada gudumuwar Naira biliyan 2.1 ga jihohin da bukata ta taso masu a fadin kasar nan.

Punch ta bi yadda gwamnan ya raba gudumuwa daga watan Junairun 2021 zuwa Oktoban nan.

1. Jihar Sokoto

A lokacin da gobara ta ci babbar kasuwar Sokoto, Gwamnan Ribas ya tallafawa Gwamna Aminu Tambuwal da kyautar N500m a ranar 10 ga Junairun 2021.

Kara karanta wannan

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Gwamna Atiku Bagudu mai makwabtaka da Sokoto, ya ba ‘yan kasuwar gudumuwar N30m a lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Jihar Akwa Ibom

Nyesom Wike ya bada kyautar N600m ga jihar Akwa Ibom a Mayun 2021. Gwamnan ya bada kudi wajen gina asibitin koyar da likitoci da ke Awa a garin Onna.

Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike da Sarkin Musulmi Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

3. Jihar Bayelsa

Kokarin gwamnan bai tsaya nan ba, ya bada N500m domin a gina jami’ar aikin likitanci a garin Yenagoa. An yi wannan a watan Fubrairun shekarar nan.

4. Jihar Kaduna

Da Gwamnan ya zo Kaduna domin yakin neman zama ‘dan takaran PDP a 2023, ya bada gudumuwar N200m domin kula da wadanda rikicin ‘yan bindiga ya ci.

5. Jihar Legas

A makon jiya Nyesom Wike ya ziyarci Legas, nan ma ya raba N300m ga matan jami’an gwamnatin Legas, yace ya yi hakan domin yabawa ayyukan da ake yi.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

Lissafin LP a zaben 2023

Kun ji labari takarar Peter Obi a zaben sabon shugaban kasa tana cigaba da motsa siyasa, musamman ganin yadda Obi ya samu karbuwa a Kudancin Najeriya.

Ana hasashen Jam’iyyar Labour Party za ta gwagwiyi kuri’un da Atiku Abubakar ya samu a 2019. Wannan tasiri zai iya aiki har a wasu jihohin da ke Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel