Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su

Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su

  • Gwamnatin tarayya ta kwaso yan Najeriyan da gwamnatin kasar UAE ta fiitittika daga kasar amma basu da hanyar dawowa gida
  • Yan Najeriya guda 542 sun dira Najeriya cikin jirgin shata da safiyar Lahadi, 23 ga watan Oktoba
  • Gwamnatin kasar UAE tace daga yanzu ta haramta baiwa yan Najeriya biza sai baba ta gani

Abuja - Bayan makonni ana tattaunawa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta kwaso yan Najeriya 542 da aka dora daga kasar hadaddiyar daular Larabawa UAE ranar Lahadi.

Yan Najeriyan sun dira tashar jirgin Nnamdi Azikwe cikin jirgin shata da akayi musu ta Max Air.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), wadanda aka kwaso sun hada da maza 79, mata 460, da kananan yara 3, rahoton Channels.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

NIDcom
Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su Hoto: @nidcom_gov
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka karbi bakuncinsu

Yayinda suka dira Najeriya, jami'an kiwon lafiya sun tantancesu, hukumomi daban-daban sun tantancesu kuma hukumar shiga da fice ta tantancesu kafin NEMA ta basu kudin mota $100 na tafiya gida.

Dirakta Janar na hukumar NEMA, Mustapha Habib Ahmed, wanda ya karbi bakuncinsu a madadin gwamnatin tarayya ya basu shawara su koyi darasi da wannan abu.

Shugaban NEMA wanda ya samu wakilcin Dirkatan sashen kudi, Alhaji Sani Ahmed Jiba, yace gwamnati ta amince a basu dan kudi da zai taimaka musu wajen tafiya gidajensu.

Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya

Mun kawo muku cewa Hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar Juma'a ta yanke shawarar haramtawa yan Najeriya Biza shiga birnin Dubai gaba daya.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari Zai Shilla Kasar Koriya Ta Kudu Gobe

A wasikar sanarwar da gwamnatin ta yiwa abokan hukdanta irinsu kamfanonin jirage da dillalan tafiya, gwamnatin kasar ta ce daga yanzu duk wanda ya nemi biza ba za'a bashi ba, rahoton Tribune.

A cewar wasikar:

"Wannan sabuwar doka ta shafi dukkan yan Najeriya a wannan lokaci."
"Ku baiwa kwastamominku shawara su sake bada takardar C2=AO idan aka sulhunta tsakanin Gwamnatin Najeriya da Na mu."

Har yanzu dai basu bayyana takamammen dalilin yin haka ba.

Dubai ya kasance daya daga cikin garuruwan da yan Najeriya ke zuwa don yawon bude ido, shakatawa, da kasuwanci.

Da farko, Sakamakon rikicin da yan Najeriya ke yi a Dubai, gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta gindaya sabbin sharruda wa yan Najeriya.

Rahotanni sun nuna yadda wasu yan Afrika da ake zargin yan Najeriya ne ke haddasa rikici a kasar Dubai kuma an fitittiki da dama cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel