Yan Sanda Sun Kama Kwamandan IPOB/ESN, Sun Lalata Sansanonin Horar da Tsageru a Ebonyi
- Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta bayyana irin aikin kirkin da ta yi wajen ragargazar 'yan ta'addan IPOB
- An kame wani kasurgumin kwamandansu tare da wasu da dama, kana an gano makamai da kayan aikata barna
- Kungiyar IPOB dai itace mai fafutukar ballewa daga Najeriya tare da kafa sabuwar kasa mai suna Biafra
Jihar Ebonyi - 'Yan sandan jihar Ebonyi sun yi nasarar kame wasu mambobin kungiyar nan ta ta'addanci IPOB da sojojinta ESN bayan wani samamen da ta kai kan wasu sansanonin horar da tsageru.
'Yan sandan sun bayyana cewa, wadannan sansanoni na tsageru suna cikin wani duhun daji ne na kauyen Omege a lardin Agba ta karamar hukumar Ishielu ta jihar, The Cable ta ruwaito.
Chris Anyanwu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya kuma bayyana cewa, jami'ai sun kwato makamai da alburusai da kakin sojoji da dai sauran kayayyakin aikata laifi.
A cewar sanarwar da kakakin ya fitar, ta ce an samu nasarar kai wannan samame ta hanyar amfani da bayanan sirri daga jami'an DSS, sojoji da sauran jami'an dabaru na hukumar 'yan sanda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazakila, ta ce an kama wani kasurgumin kwamandan haramtacciyar kugiyar Nnamdi Ngwuta da kuma wani fitaccen mambansu da ake kira Felix Ogudu.
Sanarwar ta ce:
"Yayin kaiwa ga sansanonin, gamayyar jami'ai sun yiwa 'yan ta'addan kwanton bauna da ruwan harbi ta kowane bangare.
"Ba tare da wani bata lokaci ba, tawagar dake biye ita ma ta kutsa a hakan, kuma tabbas wutan da suka rike ya fi karfin tsagerun."
A bangaren 'yan ta'addan, rundunar 'yan sanda ta ce, tuni suka fara rera wakar yaki tare da tserewa ta rafin Opeke da kwakwalwalin dake gefensa don neman tsira.
An hallaka 'yan ta'adda da dama, an lalata komai nasu
Sai dai, duk da haka an hallaka 'yan ta'addan da dama, inji rahoton Tribune Online.
Bayan lallasa 'yan ta'addan, jami'an tsaro sun kuma lalata sansanin horon da tsagerun ke kira “IGBO BU IGBO TRAINING SCHOOL CAMP”.
A cewar sanarwar:
"Hakazalika, wata gadar katako da suke ginawa, wacce za ta taimakawa tsageru wajen shige da fice, ita ma an wargazata."
A bangare guda, kakakin 'yan sandan jihar ta Ebonyi ya bayyana adadin kayayyakin da aka kwato da suka gada da sulken bindiga 11 da kakin soja guda takwas.
Hakazalika, an kwato gas din girki, harsasan FNC guda 110, harsasan GPMG guda 40, na'urar sarrafa nakiyar EOD guda biyu, keken bindiga guda biyar da kuma bindigogi masu tashi daya guda biyar.
An Tsige DPO Daga Kujerarsa Bayan Sheke Wanda Ake Zargi da Farmakar Fasto Sulaiman
A wani labarin, kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, AIG Abutu Yaro ya cire DPO na yankin Auchi, CSP Ayodele Suleiman daga kujerarsa bisa laifin kashe wanda ake zargin da aka kama kan kai farmaki a tawagar fasto Johnson Suleiman, mai kula da cocin Omega Fire Ministry.
Hakazalika, an umarci jami'in da ya gaggauta mika kansa ga hukumar 'yan sanda domin ba da bahasi kan abin da ya faru, rahoton Punch.
A cikin wata sanarwa da mai taimakawa kakakin hukumar na jihar, Jennifer Iwegbu ta fitar, ta ce, cire DPOn na daga matakan gano dalilan da suka kai ga mutuwar daya daga wadanda suka farmaki ayarin faston.
Asali: Legit.ng