Sharruda 5 Da Kasar Dubai Ta Gindayawa Duk Dan Najeriya Mai Son Zuwa Yawon Bude Ido

Sharruda 5 Da Kasar Dubai Ta Gindayawa Duk Dan Najeriya Mai Son Zuwa Yawon Bude Ido

Sakamakon rikicin da yan Najeriya ke yi a Dubai, gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta gindaya sabbin sharruda wa yan Najeriya.

Dubai ya kasance daya daga cikin garuruwan da yan Najeriya ke zuwa don yawon bude ido, shakatawa, da kasuwanci.

Rahotanni sun nuna yadda wasu yan Afrika da ake zargin yan Najeriya ne ke haddasa rikici a kasar Dubai kuma an fitittiki da dama cikinsu.

Shugabar hukuma yan Najeriya mazauna kasashen waje ya zayyana jerin sharrudan da gwamnatin UAE ta gindaya yanzu.

A cewarta, ba za'a baiwa dan Najeriya Biza ba sai ya cika wadannan sharruda.

Dubai
Sharruda 5 Da Kasar Dubai Ta Gindayawa Duk Dan Najeriya Mai Son Zuwa Yawon Bude Ido

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga jerinsu:

1. Dole sai ka kasace mai shekaru akalla 40

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

2. Dan kasa da shekaru 40 sai da ya tafi da iyalinsa, za'a bashi 'Family Visa'

3. Sai ka nuna hujjan cewa ka kama Otal ko wani wajen zama a UAE

4. Zai ga gabatar da takardan hada-hadan bankin na watanni 6 (Bank account Statement)

5. Sai ka nuna cewa ka sayi tikitin dawowa Najeriya

Daga Yanzu Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Mai Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasarta, FG

Gwamnatin Tarayya tayi tsokacin kan halin da wasu yan Najeriya suka shiga yayinda aka taresu a tashar jirgin Dubai, haddadiyar daular Larabawa kuma aka hanasu shiga.

A faifan bidiyon, yan Najeriyan na kukan yadda aka hanasu shiga kasar UAE duk da mallakar biza.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da jawabi kan wannan lamari.

Kakakin ma'akatar, Francisca Omayuli, yace laifin yan Najeriyan ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel