Abba Kyari: Yadda na Biya Cin Hanci Wajen Shigo da Hodar Iblis Inji Shaida a Kotu

Abba Kyari: Yadda na Biya Cin Hanci Wajen Shigo da Hodar Iblis Inji Shaida a Kotu

  • Lauyan hukumar NDLEA ya kira Emeka Ezenwanne ya bada shaida a shari’ar da ake yi a kotun tarayya
  • Yanzu haka Emeka Ezenwanne yana garkame a gidan gyaran hali tun da aka kama shi da kwayoyi
  • Mai laifin ya fadawa kotu yadda ya biya cin hanci a filin jirgi domin ya sulale da kwayoyi daga kasar waje

Abuja - Wani da aka kama da laifin safarar hodar iblis, Emeka Ezenwanne ya bada shaida a kotun tarayya na garin Abuja a shari’ar NDLEA da Abba Kyari.

Premium Times tace Ezenwanne ne shaida na biyar da hukumar NDLEA ta gabatar, ya kuma yi bayanin yadda ya bada cin hanci wajen shigo da kwayoyi.

Kamar yadda Ezenwanne ya fadawa kotu da bakinsa, ya ba jami’an tsaron da ke aiki a filin jirgin Akanu Ibiam N10, 000, domin ya wuce dauke da hodar iblis.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Basarake Ya Zage Yana Yi wa Bola Tinubu da Gwamnan APC Kamfe

Wannan mutum wanda yanzu yana daure a gidan yari da ke garin Suleja, yace an dauko hodar iblis din ne daga kasar Brazil, aka biyo da shi ta Habasha.

Mai bada shaidar ya fadawa Lauyan NDLEA, Joseph Sunday cewa ya je birnin Addis Ababa a tsakiyar Junairu domin ya karbo kwayoyi daga kasar Brazil.

“A ranar 16 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:30 a agogon kasar Habasha, jirgin da ya zo daga Brazil ya sauka. Jim kadan bayan nan aka kira ni a waya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin farko da ya kira ni a wayar salula, ana kiransa ‘Alhaji’.”

- Emeka Ezenwanne

Filin jirgi
Filin jirgin Akanu Ibiam Hoto: www.skyscrapercity.com
Asali: UGC

“A ranar 19 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:00 na safiya, muka hau jirgin da zai sauka filin sauka da tashin jiragen sama da ke garin Enugu.
Da muka isa filin jirgi, na fito na zauna a mota, ina jiran wanda muke tare da shi (Umeibe), ya fito.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Daga nan aka fara samun matsala, ‘yan sanda a cikin fararen kaya da muka gane cewa dakarun IRT ne, suka tare kayan da Umeibe ya dauko.
A filin jirgin saman Enugu, an bukaci In biya kudi ga mutanen da za su duba jaka ta. Saboda haka sai na biya su N10, 000, suka kyale ni na wuce.

- Emeka Ezenwanne

IRT sun ankarar da NDLEA

Vanguard ta rahoto Ezenwanne yana cewa daga baya 'yan sandan suka fito da rigunansu, sai ya fahimci 'yan IRT ne, a karshe suka cinna shi ga NDLEA.

Da aka zo gaban jami’an NDLEA, Ezenwanne yace adadin kwayoyin da suka shigo da su ya ragu, amma yace duk abin da aka yi, bai hau da DCP Abba Kyari ba.

Mai binciken Kyari ya mutu

Kwanaki kun ji labari Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

Marigayi DIG Egbunike ne jami’in da IGP ya ba alhakin gudanar da bincike a kan DCP Abba Kyari. A halin yanzu an dakatar da Kyari, ana yin bincike a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng