An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

  • A karon farko a tarihin kafuwar Najeriya, an samu jihar da ta fara cin arzikin man fetur daga Arewa
  • Gwamnan jihar Kogi ya tabbatar da cewa sun karbi 13% da ake warewa jihohin da ke hako danyen mai
  • RMAFC ta fara lissafi da jihar tsakiyar Arewacin Najeriyar ne bayan hako danyen rijiyar man Ibaji

Kogi - Maganar da ake yi, jihar Kogi ta samu kasonta na farko a matsayin jiha mai arzikin man fetur a Najeriya, a karon farko a Arewacin kasar nan.

Jaridar The Nation ta rahoto Gwamna Yahaya Bello yana bayanin cewa gwamnatin jiharsa ta karbi kaso daga cikin 13% da ake warewa jihohi masu mai.

Mai girma Yahaya Bello ya yi wannan bayani a wajen taron majalisar zartarwa na jiha wanda aka saba yi duk mako a gidan gwamnati na Lugard House.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Gwamna Bello yace gwamnatinsa tayi abubuwan a-zo-a-gani, inda yace samun arzikin mai zai taimaka wajen cigaba da kawowa mutanensa cigaba.

A jawabinsa, Daily Trust tace Gwamnan ya nuna farin-ciki da wannan nasara da jihar ta samu.

A cewar Bello, gwamnatinsa ta samu lambar yabo da kyauttuka iri-iri saboda yadda suke tafiyar da mulki keke-da-keke kuma cikin gaskiya da amana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kogi
Gwamnan Kogi a Fadar Aso Rock Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

“Mun sha wahala wajen kafa tarihin nan. Ba don gudumuwar mutanenmu da suka tsaya mana ba, da ba za mu iya kai wa ga nasarar nan ba.
Muna mika godiyarmu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da jagorancin da ya yi, da kuma RMAFC da ta sa wannan ya tabbata.”

- Yahaya Bello

Al'umma za su amfana da dukiyar

Gwamnan ya yi alkawarin amfani da dukiyar da aka samu wajen gina makarantu, asibitoci, da tituna, sannan a tallafawa marasa karfi tare da inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gwamnatin Buhari ta gani makarantun bogi 349 a jihar Arewa dake cinye kudin ciyar da dalibai

Kwamishinan yada labarai na jihat Kogi, Kingsley Fanwo yace kudin sun fara zuwa ne a lokacin da Gwamna yake yin ayyukan da za a tuna da shi nan gaba.

Ya aka yi Kogi ta samu kudin?

Hukumar RMAFC mai kasafin dukiyar kasa da albashi ta sa Kogi a matsayin jihar da take da arzikin mai, don haka za ta rika amfana da kashi 13% duk wata.

Dama can an yi alkawari jihar za ta fara karbar kasonta a wannan kudi idan rijiyar man Ibaji ya fara aiki, kuma yana kawowa asusun tarayya kudin-shiga.

Gwamnan Kwara ya nada Hadimai

An samu rahoto a ranar Alhamis cewa mata 16 suka samu kujerun Masu taimakawa Mai girma Gwamna jihar Kwara wajen ganin cin ma manufofin SDGs.

A yanzu mata suke rike da 56.25% na kujerun Kwamishinoni da kuma 50% na mukaman Sakatarorin din-din-din a mulkin Abdulrazaq Abdulrahman.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng