Yan Sanda Sun Musanta Jita-Jitar Kai Hari Kan Ayarin Motocin Bola Tinubu a Osun

Yan Sanda Sun Musanta Jita-Jitar Kai Hari Kan Ayarin Motocin Bola Tinubu a Osun

  • Hukumar yan sandan jihar Osun ta musanta wani rahoto da ake yaɗa cewa cewa wasu matasa sun farmaki Bola Ahmed Tinubu
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Olawale Olokode, yace Bidiyon da ake yaɗa ba na yanzu bane
  • A wata sanar da kakakin yan sandan ya fitar, tace Bola Tinubu bai halarci wani taro a jihar Osun ba kwanan nan

Osun - Rundunar yan sanda reshen jihar Osun ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa an farmaki Ayarin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu a ƙarshen makon nan.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa rundunar ta musanta jita-jitar ne a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya fitar.

Bola Ahmed Tinubu.
Yan Sansa Sun Musanta Jita-Jitar Kai Hari Kan Ayarin Motocin Bola Tinubu a Osun Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa labarin da Bidiyon da ake yaɗa wa ake jingina shi ga Ayarin Tinubu ba na yanzu bane, farmaki ne da aka kaiwa ayarin gwamna Oyetola lokacin zanga-zangar EndSARS ranar a watan Oktoba, 2020.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Umarci Ciyamomi 20, Mataimaka da Wasu Kusoshin Gwamnati Su Sauka Daga Kujerunsu

Sanarwan tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An jawo hankalin hukumar yan sanda kan wani labari da Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta mai nuna cewa matasan Osun sun farmaki ayarin Sanata Bola Tinubu ranar 8 ga watan Oktoba, 2022."
"Hukumar yan sanda na sanar da ɗaukacin al'umma cewa labarin da Bidiyon wani hari ne da aka kai wa Ayarin gwamnan Osun, Oyetola Adegboyega, lokacin zanga-zangar EndSARS shekara biyu da suka gabata, 17 ga Oktoba, 2022."
"Kwamishinan yan sanda, Olawale Olokode, na sanar wa mutane cewa labarin ba haka yake ba kuma ya saɓa, wanda wasu gurbatattun mutane ke yaɗa shi da nufin ta da hankula."

Tinubu bai ziyarci jihar Osun ba kwanan nan - CP

Hukumar yan sandan ta kara da cewa tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, bai halarci wani taro a jihar Osun ba kwanan nan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ba Ta Da Halastacen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Ku Zabi Atiku, PDP Ga Yan Najeriya

"A taƙaice, Ina mai sanar muku da cewa Sanata Bola Ahmed Tinubu, bai zo jihar Osun ba, babu wani taro da ya halarta."
"Saboda haka kwamishina na kira ga mutane su ci gaba da harkokinsu na yua da kullum ba tare da fargabar matsalar tsaro ba, yayin da duk wata ƙofa da za'a iya samun matsala an tosheta."

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Benuwai ya yi kira ga shugaban PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga mukaminsa

Samuel Ortom, gwamnan jihar da Ayu ya fito a arewa ta tsakiya, yace Ayu ya faɗa wa duniya a baya cewa zai sauka idan aka tsayar da ɗan arewa.

Gwamna Ortom ya shawarci Ayu ya ba da haƙuri idan ba zai sauka ba amma ba ya dinga cewa zangon mulkinsa na shekara huɗu bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel