An Kama Korarrun Ma'aikata Da Suka Yi Yunkurin Sace Tsohon Mai Gidansu Saboda Ya Sallame Su Daga Aiki

An Kama Korarrun Ma'aikata Da Suka Yi Yunkurin Sace Tsohon Mai Gidansu Saboda Ya Sallame Su Daga Aiki

  • Yan sanda a Jihar Ogun sun kama wasu mutane uku da suka yi barazanar za su sace tsohon mai gidansu
  • Korarrun ma'aikatan sun tura wa tsohon mai gidansu sakon kar ta kwana ne suna mai cewa ya biya su N5m ko su sace
  • Tsohon mai gidan ya yi korafi wurin yan sanda inda aka kaddamar da bincike aka kama su, sun amsa cewa sun masa barazanar ne don ba su ji dadin sallamarsu daga aiki ba

Ogun - An kama wasu maza uku kan zargin garkuwa da tsohon mai gidansu, Ifeanyi Olayinka bayan ya sallame su daga aiki a Ijebu-Ode, Jihar Ogun.

An kama wadanda ake zargi su ukun: Peter Nse, 24, Chuckwuma Nwobodo, 48, da Michael Umanah, 30 bayan tsohon mai gidansu ya shigar da korafi.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Ogun.
Kwamishinan Yan Sandan Jihar Ogun. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Kakakin yan sandan jihar Ogun, SP, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Oyeyemi ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan tsohon mai gidansu, Olayinka, ya kai rahoto cewa wani wanda ya kira kansa 'Killer Vagabond of Africa' ya tura masa sakon tes.

Ya ce:

"Wanda ya turo sakon ya umurci wanda ya yi korafin ya biya N5m cikin wani asusun banki idan ba haka ba kuma za su iya sace shi cikin kankanin lokaci.
"Bayan samun rahoton, DPO na Ugbeba, CSP Musiliu Doga, ya umurci jami'ansa su binciko wanda ya aika wannan mummunan sakon.
"Daga nan ne bincike ya yi sanadin kama wasu yan Anambra da ake zargi masu suna Peter Nse da Chuckwuma Nwobodo.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

"Kama su ya yi sanadin kama na ukunsu, Micheal Umanah a garin Ago-Iwoye."

Bayan an kawo su gaban wanda ya yi korafin ne ya gane su cewa tsaffin ma'aikatansa ne da ya kora ba da dadewa ba saboda wani laifi.

Sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa

Bayan an musu tambayoyi, sun amsa cewa sun aikata laifin da ake zarginsu saboda ba su ji dadin yadda wanda ya yi korafin ya kore su daga aiki ba.

Kakakin yan sandan, ya ce kwamishinan yan sanda Lanre Bankole, ya umurci a tura su sashin binciken manyan laifuka don zurfafa bincike.

Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa

Rundunar yan sandan Jihar Gombe a ranar Talata ta yi holen wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga iyalan wadanda suka sace.

Kara karanta wannan

Bakano ya girgiza intanet, ya kera keke napep din da ta ba 'yan Najeriya mamaki

A cewar kakakin rundunar, Mahid Abubakar, hakan na zuwa ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammad a Jihar Taraba, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel