Da Dumi-duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Wata Jihar Arewa
- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin kauyen Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara
- Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 1:45 na ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba bayan sun ajiye baburansu a jeji
- Yan bindigar sun kuma kai hari kauyen Msama-Mudi da ke makwabtaka da karamar hukumar Bukkuyum inda suka sace masu jego 8 da matasa hudu
Zamfara - Wasu guggun yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin kauyen Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba, HumAngle ta rahoto.
An sace hakimin mai suna Marafa Danbaba da misalin karfe 1:45 na rana a gidansa da ke karamar hukumar Gummi bayan sun farmaki kauyen.
A cewar wasu da abun ya faru kan idanunsu, maharani sun ajiye baburansu a cikin jeji kafin suka taka zuwa kauyen sannan suka farmaki gidansa.
Matsalar rashin tsaro a Zamfara na ci gaba duk da agajin da rundunonin tsaro ke kaiwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Asabar, an sake kai wani hari a kauyen Msama-Mudi da ke makwabtaka da karamar hukumar Bukkuyum.
A yayin farmakin, maharan sun nemi wani manomi da suka samu yana hutawa a karkashin bishiya da ya nuna masu gidajen masu kudi a garin.
Wani malamin makaranta mai suna Mustapha Mamman yace:
“Yan ta’addan sun tursasa Lauwali Dan-tawasa nuna masu gidajen masu kudi a kauyen. Amma ya fada masu cewa bai san su ba. Hakan da yayi yasa sun sace dansa.”
Sauran mutanen da aka sace a harin sun hada da masu jego takwas da wasu matasa maza su hudu.
A cewar Musa Isah Masama, an ajiye jinjiri dan wata biyar a kasa yayin da aka sace mahaifiyarsa.
Surukin hakimin da aka sace a ranar Lahadi, Ibrahim Aminu ya ce sun lura da yawan sa ido.
Jagoran karamar hukumar Gummi, Abubakar Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a Iyaka yana mai cewa zuciyarsa tayi nauyi da samun mummunan labarin.
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Wata Jiha
A wani labarin, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Hon. Lucky Okechukwu, shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Igboeze ta kudu da ke jihar Enugu, rahoton Sahara Reporters.
Koda dai babu cikakken bayani kan lamarin, an tattaro cewa an harbe Okechukwu ne har lahira a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba a garin Unadu.
Wani jigon jam’iyyar a jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a bashi umurnin magana ba, ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng