Gwamnatin tarayya ta rabawa masu kanana da matsakaitan sana'o'I Naira 18 biliyan a Oyo
Bankin nan na sana'oi da kasuwanci mallakin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ya rarraba akalla Naira 18 biliyan daga cikin Naira 20 biliyan ga kanana da kuma manyan masana'antu da aka ware a jihar Oyo.
Shugaban bankin dai mai suna Mista Olukayode Pitan shine ya sanar da hakan yayin da ya jagoranci tawagar bakin zuwa wata ziyarar bangirma da suka kai wa gwamnan jihar ta Oyo a ofishin sa.
KU KARANTA: Kotu ta dage shari'ar Dasuki har sai watan Maris
Legit.ng dai ta samu cewa shugaban bankin ya kuma bayyana cewa gwamnatin nan ta shugaba Buhari a shirye take wajen ganin ta taimakawa dukkan masu so suyi sana'a a ko ina suke a fadin kasar nan.
Haka ma dai Kamar dai yadda muke samu daga majiyar mu shine tsohon kwamishinan labarai da tsare-tsare a jihar Abia Dakta Anthony Agbazuere ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar PDP a zuwa jam'iyya mai mulki a gwamnatin tarayya ta APC.
Kamar yadda muka samu, Dakta Anthony Agbazuere ya bayyana cewa rashin kyakkyawan tsari na gudanar da jam'iyyar ta PDP ne ya sa ya bar ta.
Legit.ng ta samu cewa Mista Anthony Agbazuere ya bayyana cewa yanzu zama a jam'iyyar ta PDP ya zamar masa wani abu mai wahala musamman ma ganin yadda wasu mutanen da ya kira masu hana ruwa gudu sun shiga jam'iyyar sun kuma hana harkokin mulki gudana yadda ya kamata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng