Zaben 2023: Ku Sake Bawa APC Wata Damar, In Ji Dr Kailani Muhammad
- Dr Kailani Muhammad, dan gwagwarmayar siyasa kuma mai sharhi kan al'amuran da suka shafi mutane ya roki yan Najeriya su sake zaben APC
- Shugaban na kungiyar 'Network for Election Education, Sensitization and Awareness' ya ce APC ta samu nasarori cikin shekaru bakwai da suka shude
- Kailani ya ce duk da cewa an fuskanci wahalhalu da kallubale, gwamnatin Buhari ta samu gaggarumin nasara a bangaren tsaro, samar da ayyukan more rayuwa da sauransu
Kaduna - Wani dan gwagwarmayar siyasa kuma mai sharhi kan al'amuran da suka shafi al'umma, Dr Kailani Muhammad, ya ce yan Najeriya su duba yiwuwar sake dawo da APC kan mulki saboda nasarorin da ta samu a shekaru bakwai da suka shude.
Kailani, wanda kuma shine shugaban kungiyar wayar da kan mutane kan zabe wato 'Network for Election Education, Sensitization and Awareness' ya yi wannan jawabin ne a Kaduna, Vanguard ta rahoto.
Gwamnatin Buhari ya karya lagwon Boko Haram da masu garkuwa
Yayin da ya ke jinjinawa gwamnatin Buhari, dan gwagwarmayar siyasar ya yi bayanin cewa gwamnatin mai ci yanzu ta yi nasarar ragargazan Boko Haram, yayin da kuma tana kan magance yan bindiga, masu garkuwa musamman a arewa maso yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Babu shakka, kasar ta yi fama da kallubale amma duk da haka, an samu manyan nasarori a bangaren tsaro, tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da wasu bangarorin cigaba.
"Muna fata za a sake yin zabe lafiya a Najeriya kuma a samu gwamnatin za ta cigaba da ayyukan alherin da gwamnatin APC ta fara."
Za mu wayar da kan masu zabe
Kailani, ya yi bayanin cewa kungiyarsa a shirye ta ke ta wayar da kan al'umma da ilmantar da su kan muhimmancin kuri'unsu, ya kara da cewa ya kamata yan kasa su tabbatar an kirga kuri'unsu.
Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi APC a 2023 don samun damar ci gaba da ganin irin ayyukana
A wani rahoton, Shugaban Buhari ya bukaci al’ummar kasar nan da su zabi APC a zabe mai zuwa domin tabbatar da dorewar harkokin siyasa, da kwanciyar hankali a kasar da ma yankin yammacin Afrika, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma’a a lokacin da yake karbar tawagar daga jihar Nasarawa karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule a fadar gwamnati da ke Abuja, a cewar sanarwar da fadarsa ta fitar.
Asali: Legit.ng