Bankin CBN Zai Fara Cire Kudi Daga Asusun ’Yan Najeriyan da Suka Ci Bashin Gwamnati
- Babban Bankin Najeriya ya ce zai fara cire kudi daga asusun bankin 'yan Najeriyan da suka taba cin bashin gwamnati na noma
- Hakzalika, bankin zai cire kudi daga asusun gwamnatin wasu jihohi domin biyan bashin da aka ba su
- An ba 'yan Najeriya da dama rancen kudi karkashin shirye-shirye da dama na noma a kasar nan
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara zare kudade daga asusun bankin gwamnatin jihohi da wasu 'yan Najeriya domin warware bashin da ake binsu.
Daraktan raya fannin kudi na CBN, Yusuf Yila ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, The Cable ta ruwaito.
Yila ya ce babban bankin ya shirya karbo kudade daga gwamnati jihohi da manoma ne da suka ci gajiyar kowane daga shirye-shiryen rance na gwamnati tarayya.
Duk da cewa bai ambaci jihohin da ake bi bashin ba, Yila ya ce babban bankin kasa ta hannun asusun rarraba kudaden jihohi na FAAC ya fara ciran kudaden da ake bin jihohin a kowane wata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bayyana cewa, babban bankin zai cire kudin ne na tsawon watanni shida kacal.
Bayani kan wadanda suka ci rancen shirin Anchor (ABP)
A cewarsa, wanda suka ci bashin CBN a karkashin shirin noma na ABP da CAC na daga cikin wadanda shirin zai shafa.
A kalamansa:
"Kowane mutum ko jihar da ta karbin rancen ABP za ta biya. Muna da BVN dinsu.
"Wadannan mutanen kananan manoma ne da suka karbi kudi domin noma daga gwamnatin jihohi karkashin AVP, amma har yanzu basu biya ba."
Hakazalika, ya ce CBN ya fara magana da hukumar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) magana wajen tabbatar da dawo da kudaden rancen.
Ya kuma bayyana cewa, ba da rancen bai ba da fa'ida kamar yadda gwamnati ta nufa ba, The Nation ta ruwaito.
Wani ma'aikacin CBN da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, akwai shirye-shirye na gwamnati da dama kan harkar noma, amma ba za a iya ci gaba da yinsu ba saboda rashin tasirin ba da tallafin.
Babu Wata Jiha da Aka Ba Izinin Mallakar Makamai Masu Sarrafa Kansu, Martanin Fadar Buhari Ga Gwamna Akeredolu
A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta ce, babu wata jiha a Najeriya da ke da ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu kamar dai bindigogi kirar AK47, TheCable ta ruwaito.
Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar a yau Talata 27 ga watan Satumba.
Gwamnati ta ce, mallakar bindiga kirar AK47 matukar ba a hannun jami'an tsaro bane to tabbas ya saba doka, kuma akwai hukunci a kai.
Asali: Legit.ng