Yan sanda sun kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Yan sanda sun kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama shugaban kungiyar da sukayi garkuwa da fararen fata hudu a makon da ya gaba a jihar Kaduna.

Yan kwanaki kadan bayan ceto yan kasar waje, yan sanda sun cika alkawarinsu a ranar Laraba, inda suka kama shugaban kungiyar a yankin Kagarko dake jihar Kaduna.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tawagar sufeto janar na yan sanda ne suka kama mai laifin yayinda suka samo bindigogin AK 47 daga hannun shi.

Dan ta’addan wanda aka ambata da suna Dogo Russia, ya tona asirin kashe yan sandan tafi da gidanka da aka jona da bakin wajen kafin su sace su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mutane 4 sun mutu, 10 sunji rauni, sannan an sanya ma gidaje wuta yayinda makiyaya suka kai hari jihar Plateau

A ranar Talata da ta gabata ne yan bindiga suka sace bakin hudu da aka ceto, Amurkawa biyu da kuma yan kasar Kanada biyu a jihar Kaduna.

Yan sanda ne suka ceto su kwanaki hudu da da sace su a yankin Jere dake karamar hukumar Kagarko na jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng