Gwamnatin Buhari Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Janye Umarnin da Ta Bayar Na Bude Jami’o’i

Gwamnatin Buhari Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Janye Umarnin da Ta Bayar Na Bude Jami’o’i

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana janye batun da ta yi na kira ga a bude jami'o'in kasar duk da yajin da ASUU ke yi
  • Kungiyar ta shafe watanni sama da shida tana yaji, batun ya yi kamari har an je gaban kotu amma ba a samu mafita ba
  • Dalibai a Najeriya sun fara neman mafita da kama sana'a tun bayan da yajin aikin ya tumbatsa a kasar

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) a yammacin yau Litinin 26 ga watan Satumba ta janye umarnin da ya ba shuganannin jami'o'i na su koma bakin aiki, Vanguard ta ruwaito.

A wani rahoton da muka samo da sanyin safiyar yau, an wata wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da NUC ta fitar ta umarci shugabannin jami'o'in gwamnati a Najeriya da su bude makarantu tare da kiran dalibai su dawo makaranta.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Wutar Lantarki Ta Dauke A Najeriya Gaba Daya Da Safiyar Nan, 0 Megawatt

Gwamnati ta janye umarnin bude jami'o'in Najeriya
Gwamnatin Buhari Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Janye Umarnin da Ta Bayar Na Bude Jami’o’i | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai, a wata sabuwar wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/136, hukumar ta NUC ta janye batun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da hukumar bata bayyana dalilin bayyana janye umarnin ba, ta dai ce daga baya za ta yi magana game da duk wani ci gaba da aka samu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda yajin aikin ASUU yake

Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta shiga yajin aiki tun watan Fabrairun bana, ta shafe watanni sama da shida jami'o'i a garkame.

An sha zama da kungiyar amma ba a samu mafita ta kai tsaye ba, lamarin da ke kara tunzura gwamnati.

Gwamnati ta kai karar ASUU kotu, inda aka umarci kungiyar da ta koma bakin aiki cikin gaggawa.

Sai dai, kungiyar ta tubure, ta daga kara kana ta yi watsi da batun kotu.

A yau kuma, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami'o'i (NUC) ta umarci shugabannin jami'a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu.

Kara karanta wannan

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.

Jaridar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami'o'i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel