Yan Fashi Sun Kai Wa Direktan Shahararren Gidan Talabijn Da Rediyo A Najeriya Hari A Abuja
- Wasu bata garin sun kai wa Mr Mac Imoni Amarere, babban direkta a DAAR Communication hari a birnin tarayya Abuja
- Maharan sun yi wa direban Amarere rauni sannan shi kuma suka kwace masa abubuwansa masu daraja yayin harin
- Kungiyar yan jarida ta Najeriya reshen DAAR Communication sun yi tir da harin kuma sunyi kira ga yan sanda su kara yawan jami'ansu da ke sintiri a tituna
FCT, Abuja - Kamfanin Sadarwa na DAAR Communication Plc, a ranar Talata ta koka kan harin da aka kai wa babban direkanta, Mac Imoni Amarere, rahoton The Punch.
An rahoto cewa, an kai wa mai gabatar da shirin Peoples-Politics-Power a gidan talabijin na AIT hari aka masa fashi yayin da ya ke bin dokokin titi kusa da makaranar Community Staff School, Asokoro, Abuja, yammacin ranar Litinin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kungiyar yan jarida na Najeriya reshen DAAR Communications Plc ta tabbatar da afkuwar lamarin cikin wani sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta ce:
"An janyo hankalin kungiyar yan jarida na Najeriya, reshen DAAR, kan afkuwar hari ga shugaban mu na DAAR Media Academy kuma jagoran shirin Peoples-Politics-Power a AIT, Mac Imoni Amarere.
"An kai wa Amarere hari ne aka masa fashi yayin da ya tsaya bin dokar titi kusa da Community Staff School, Asokoro, mallakar DSS a Asokoro, a yammacin ranar Litinin, 26 ga watan Satumba.
"Ba a masa rauni ba amma ya rasa abubuwansa masu muhimmanci, an yi wa direbansa rauni kadan. Ana jan hankulan abokan aiki su kara takatsantsan idan sun tsaya bin dokar titi a birnin, musamman da dare.
"Ana kira ga yan sanda su kara yawan shinge da masu sintiri musamman a wuraren da ake aikin titi da latarki mai tsayar da motocci. Muna kira ga abokan aiki su cigaba da kula da kansu da saura."
Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi
A wani rahoton, wasu da ake zaton 'yan fashi da makami ne ɗauke da bindigu sun farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.
Yan Fashin, adadin mutum 20, an ce sun shiga garin da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Da farko suka farmaki bankin UBA, daga nan suka zarce Bankin Zenith, daga bisani suka mamaye First Bank.
Asali: Legit.ng