FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta

FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta

  • Alamu na nuna cewa gwamnatin Najeriya zata kwace lasisin kungiyar ASUU a matsayinta na kungiyar kwadago a Najeriya
  • Sanata Chris Ngige ya sanar da cewa kungiyar ta kwashe shekaru bata kawo bayanin yadda ta kashe kudinta
  • Ya sanar da cewa, baya son tada batun ne ana tsaka da rikici tsakaninta da gwamnatin tarayya kada a siffanta hakan da bi-ta-da kulli

FCT, Abuja - Alamu sun bayyana a ranar Laraba cewa gwamnatin tarayya na iya janye rijistar kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a matsayin kungiyar kwadago sakamakon gazawarta na gabatar da rahotonta na tantancewa kamar yadda doka ta tanada a shekaru biyar da suka gabata.

Tuni dai aka bayyana cewa, magatakardar kungiyar kwadagon ya rubutawa kungiyar takardar tuhuma kan dalilin da ya sa ba za a janye satifiket din rijistar ta ba saboda taka doka, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Sanata Chris Ngige
FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta. Hoto daga thecable.ng
Asali: Twitter

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da malaman jami’o’i a fannin likitanci suka nemi ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta Najeriya da ta yi musu rijista a matsayin kungiyar kwadago ta daban a karkashin kungiyar Nigerian Association of Medical and Dental Academics, NAMDA.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta kara da cewa ba ta shiga yajin aikin da uwar kungiyar ASUU ta shiga ba, sai dai an hana mambobinta shiga makarantun ne saboda rikicin yajin aikin kungiyar ASUU.

Ta ce nan ba da dadewa ba za a fara jarrabawar daliban aji 500 da 400 na daliban likitanci, inda ta ce kasar na da karancin likitoci, kuma ba zai amfanar da ita ta yi kasa a gwiwa ba har tsawon shekara guda tana bata lokaci ba saboda yajin aikin.

Da yake jawabi a lokacin da yake karbar bakuncin mambobin NAMDA, wadanda suka ziyarce shi domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin tarayya kan kungiyar yajin aikin ASUU, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya amince da karbar bukatar kungiyar na yin rijista.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Daliban Najeriya sun ba za ta sabu ba, basu amince ASUU ta koma aiki ba

Ministan ya koka da yadda kungiyoyin da ke jami’o’in suka kasance marasa bin dokar da ta kafa dangane da gabatar da bayanin kashe kudin asusunsu na shekara-shekara.

Ya ce an takura masa ne da ya bari dokar ta sauka kan ASUU saboda yajin aikin da aka dade ana yi domin duk wani mataki da gwamnati za ta dauka za a yi kuskuren fassara shi.

Ya ci gaba da cewa, bisa ga tanade-tanaden doka, shugabannin kungiyoyin jami’o’in da ke da alhakin karbar kudaden rijista daga mambobinsu, an ba su damar yin lissafin yadda ake kashe kudaden.

El-Rufa'i Ya Ja Kunnen Dalibai, Yace Ba Zai Lamunci Rufe Hanyar Kaduna-Abuja ba

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata, ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko wata kungiya na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga ba, jaridar Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ba za a amince da wannan matakin ba, kuma wani share fage ne na karya doka da oda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel