El-Rufa'i Ya Ja Kunnen Dalibai, Yace Ba Zai Lamunci Rufe Hanyar Kaduna-Abuja ba

El-Rufa'i Ya Ja Kunnen Dalibai, Yace Ba Zai Lamunci Rufe Hanyar Kaduna-Abuja ba

  • Gwamnatin jihar Kaduna tace ba zata lamunci wasu mutane ko kungiya ta rufe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ba da sunan zanga-zanga
  • A cewar takardar da kwamishin tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, yace akwai kalubalen tsaro a hanyar
  • Ya tabbatar da cewa toshe hanyar zata iya zama wani abu daban don haka gwamnan ya jaddada cewa ba zai lamunci hakan ba

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata, ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko wata kungiya na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga ba, jaridar Guardian ta rahoto.

Kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ba za a amince da wannan matakin ba, kuma wani share fage ne na karya doka da oda.

Kara karanta wannan

Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba

Gwamna Nasir
El-Rufa'i Ya Ja Kunnen Dalibai, Yace Ba Zai Lamunci Rufe Hanyar Kaduna-Abuja ba. Hoto daga guardian.ng
Asali: UGC

Takardar tace:

“Da wannan sanarwar, ana shawartar mutane ko ƙungiyoyin da ke shirin hana zirga-zirgar ’yan ƙasa da su daina don son zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna ba ta hana ‘yan kasa ‘yancin fadin albarkacin bakinsu ba, ya zama dole ne a rika kula da harkokin tsaro da tsaron jama’a a kodayaushe.
“Haɗarin toshe hanya mai mahimmanci kamar hanyar Kaduna zuwa Abuja ba sho da amfani idan aka duba halin da ake ciki na tsaro da suka shafi hanyar da sauran wurare."
“Dole ne a mayar da hankali sosai kan yiwuwar wasu tarukan da zasu iya rikidewa zuwa tashin hankali.
“Don haka ana shawartar ‘yan kasa da su guji haifar da irin wadannan cunkoson, musamman wadanda za su yi tasiri ga al’amuran zamantakewa da tattalin arziki na sauran ‘yan kasa, ko kuma jefa rayuka cikin hatsarin da ba dole ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

"Ana tunatar da 'yan kasa cewa ya kamata a yi la'akari da tsaro kuma a bashi fifiko da muhimmanci."

- Aruwan yace.

Don haka kwamishinan ya ce kamata ya yi daidaikun mutane, kungiyoyi da sauran kungiyoyi su lura da shawarwarin da aka ba su, su kauce hanya.

Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari

A wani labari na daban, bayan da aka shafe watanni ana kai ruwa rana a batun yajin aikin ASUU, gwamnatin Buhari a ranar Talata ta ce ta yi iyakar kokarinta don ganin ta kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyar malaman jami'o'i.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Adamu Adamu a wata ganawa da ake yi da shugabannin jami’o’in tarayya da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a Abuja.

Ya zuwa yanzu dai da rahoton nan ke shigowa mana daga jaridar The Nation, an ce manyan jami'an na gwamnati suna cikin ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

Asali: Legit.ng

Online view pixel