Hukumar Lafiya Ta Ayyana Barkewar Cutar Kwalara a Jihar Gombe
- Hukumar lafiya ta jihar Gombe ta bayyana cewa, tabbas cutar kwalara ta bulla a jihar, kuma ta fara kisa a wasu yankunan
- Akalla mutane 10 ne suka mutu daga cutar kwalara a Gombe, lamarin da ya girgiza gwamnati da hukumar lafiya
- Hukumar lafiya ta bayyana matakan da take dauka domin ganin an shawo kan matsalar yaduwar cutar
Jihar Gombe - Hukumomi a jihar Gombe sun ayyana barkewar cutar amai da gudawa ta kwalara bayan da mutum 10 suka hallaka ta sanadin cutar, The Cable ta ruwaito.
Da yake zantawa da kamfanin dillacin labaran Najeriya a yau Alhamis 22 ga watan Satumba, kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Habu Dahiru ya bayyana yadda cutar ta tunbatsa a Gombe.
Dahiru, wanda sakataren hukumar lafiya ta matakin farko, Abdulrahman Shuaibu ya wakilta ya ce, a ranar 20 ga watan Satumba kadan mutum 236 ne suka kama da cutar a Gombe.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A wannan shekarar, daga watan Yuni an gano adadi mai yawa na wadanda suka kamu da cutar kwalara a karamar hukumar Balanga kuma saboda shiri da kuma daukar matakin gaggawa, an samu nasarar shawo kan lamarin.
"Cutar ta barke ne unguwanni takwas na kananan hukumomin Balanga, Yamaltu-Deba, Nafada, Funakaye da Gombe a fadin jihar.
"Hukumar lafiya ta jihar Gombe ta gaggauta kawo hanyar daukar mataki da dakilewa har ma da kula da cutar.
"Ya zuwa 20 ga watan Satumba, akwai kari matuka a adadin wadanda suka kamu da cutar, domin akalla mutum 236 ne aka gano suna dauke cutar a fadin jihar Gombe."
Dalilin hauhawar adadin wadanda suka kamu da cutar
A cewar kwamishinan, ci gaba da saukar ruwan sama da ambaliyar ruwa da ake samu na nasaba da yawaitar cutar ta kwalara a jihar.
Ya ce, za a yi rabon kwayoyin tsaftace gurbatattun rijiyoyi da bohol a yankunan da lamarin ya ta'azzara don shawo kan lamarin.
Jihohin Arewacin Najeriya na fuskantar iftila'in ambaliyar ruwan sama a watannin nan, an yi asarar rayuka da dukiyoyi, Daily Sun ta tattaro.
A cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA, sama da mutum 300 suka mutu yayin da kusan 100,000 suka rasa gidajensu ta sanadiyyar ambaliyar ruwa.
Hukumar ta ce, jihohi 29 hade da babban birnin tarayya Abuja sun yi fama da mamakon ruwa mai ambaliya a shekarar nan ta 2022.
A cewar Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Harbuwa ta Najeriya (NCDC), an samu adadin mutane 3,610 da suka kamu da kwalara a shekarar 2022 tare da mutuwar mutane sama da 91.
Ana yawan samun majinyatan amai da gudawa
Wakilin Legit.ng Hausa ya kai ziyara sashen taimakon gaggawa a asibitin kwararru na jihar Gombe, ya kuma tattauna da wani ma'aikacin lafiya, Muhammad Abdullahi.
Jami'in jinyan ya ce, ana samun masu dauke da cutar kwalara da ke zuwa daga unguwannin da ke da tazara da cikin gari, musamman a yankunan da ke da karancin ruwa.
Ya shaida cewa:
"Marasa lafiya ana kawo su kullum, wasu ciwon bai shige su sosai ba, don haka magani ake ba su ba sai an kwantar ba kawai mu sallame su.
"Kasan a Gombe akwai yankunan da ko bohol ka tona ba ya samar da ruwa, watakila rashin ruwa ke sa suke shan gurbataccen da suka samu a wadace wanda kuma yana hadari ga lafiyarsu.
"Mukam ba su shawari, idan suka debo ruwa a rijiya, ko ma bohol ne to su dafa shi, amma ka san dan adam, kuma da yawan patients (majinyara) dinmu yara ne."
Manyan Dalilai 7 Masu Hadari Zai Sa Kowa Ya Guji Cin Gandar Fatan Dabbobi
A wani labarin, yarbawa na kiransa 'Ponmo', Inyamurai kuma 'Kanda', Hausawa kuwa na cewa 'Ganda', fatar dabbobi na daga cikin abincin da 'yan Najeriya ke ci ba kakkautawa.
Gwamnati ta ce sam bai kamata jama'a suke cin wannan nau'in naman ba saboda yana rusa masana'antun fatu a kasar.
A 2019, hukumar kula da abinci da magunguna NAFDAC ta gargadi 'yan Najeriya game da cin ganda, inda tace yana da matsala ga lafiya.
Asali: Legit.ng