Hotuna: Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero Ta Kammala Karatu Da Digiri Mafi Daraja

Hotuna: Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero Ta Kammala Karatu Da Digiri Mafi Daraja

  • Matar Yusuf, Zahra Bayero Buhari ta kammala karatunta na digiri a bangaren kimiyyar gine-gine
  • Kamar yadda surukarta kuma uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta wallafa a shafinta, Zahra ta gama ne da digiri mafi daraja
  • Tuni hotunan surukarar shugaban kasar ya yadu a shafukan soshiyal midiya tare da ahlin babban jagoran kasar na daya

Surukar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Nasiru Bayero, ta kammala karatunta na digiri.

Zahra, wacce ta kasance diya ga sarkin Bichi da ke jihar Kano, Alhajin Nasiru Ado Bayero ta kammala karatunta ne a fannin kimiyyar Gine-gine da digiri mafi daraja.

Iyalan shugaban kasa
Hotuna: Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero Ta Kammala Karatu Da Digiri Mafi Daraja Hoto: aishambuhari
Asali: Instagram

Surukarta kuma uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta je shafinta na Instagram don taya matar dan nata murnar wannan nasara da ta samu.

Kara karanta wannan

Zamu Kara Albashin Ma'aikata Saboda Rayuwa Tayi Wahala: Chris Ngige

A cikin hotunan da ta wallafa, an gano Zahra tare da mijinta, Yusuf Muhammadu Buhari da kuma surukar tata, inda ta kasance sanye da kayan yaye dalibai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

“Ina tayaki murna Misis Zahra B Buhari a ranar kammala karatunki da digiri mafi daraja a bangaren kimiyar gine-gine.
“Ina maki fatan alkhairi.”

Kalli wallafar a kasa:

Legit.ng ta ji ta bakin wasu daliban Najeriya da yajin aikin ASUU ya hana su ci gaba da karatunsu.

Wani dalibi mai suna Ibrahim da ke ajin karshe a FUT ya bayyana takaicinsa kan yadda uwargidar shugaban kasar ta fito fili ta taya surukarta murnar kammala karatunta.

Ibrahim ya ce:

“Lallai wannan ya kara tabbatar da cewar ba talaka bane a gaban wadannan mutanen. Mu gamu an girkemu a gida bamu ga tsuntsu bamu ga tarko, su kuma gasu chan suna murnar kammala karatunsu a kasar waje.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Sai da Buhari Ya Kira Janar Buba Marwa ta Wayar Salula

“Idan da ace yaransu ne ke karatu a makarantun gwamnati ai ko mako biyu ba za a kai ba zasu janye yajin aiki. Yanzu mu an hanamu kammala namu karatun amma surukar shugaban kasar ta kare nata. Amma akwai Allah, wata rana sai labara.”

Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

A wani labarin kuma, shugaban masu tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa yan majalisar dokokin tarayya sun dawo daga rakiyar neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kalu ya jadadda cewa matsalar rashin tsaro wacce ita ce ta asassa kira ga tsige Shugaban kasar ta inganta sosai, Leadership ta rahoto.

A tuna cewa wasu sanatoci a fadin jam’iyya mai mulki da mai adawa sun ba Shugaba Buhari wa’adin makonni shida ya magance matsalar rashin tsaro ko a tsige shi daga kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel