Basaraken Da Aka Yi Garkuwa da Shi Ya Tsere Daga Hannun ‘Yan Bindiga a Jeji
- Sarkin Isiala Umudi a yankin Nkwere a Kudu maso gabashin da aka yi garkuwa da shi, ya dawo gidansa
- Ba tare da an biya kudi ba, Joel Nwankwo ya kubuta daga hannun miyagun da suka yi awon-gaba da shi
- Mai martaba Nwankwo ya sulale daga wani kungurmin jeji da aka ajiye shi bayan an nemi a biya N200m
Imo - Sarkin kasar Isiala Umudi a karamar hukumar Nkwerre da ke jihar Imo, Joel Nwankwo ya bar hannun masu garkuwa da mutane.
Punch ta fitar da labari a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba 2022 da ya tabbatar da cewa Joel Nwankwo ya tsira bar hannun miyagu.
Wani na kusa da Basaraken ya shaida cewa Mai martaba Joel Nwankwo ya kubuta daga dajin Okwu a garin Ikeduru, inda yake tsare.
A ranar Juma’ar da ta wuce aka dauke Nwankwo a gaban ofishinsa a garin Owerri, tun daga lokacin ne ba a sake jin wata duriyarsa ba.
Kudin fansar N200m
A karshen makon da ya wuce ‘yan bindigan da suka yi awon-gaba da Mai martaba, suka kira iyalansa domin a kawo kudin fansarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyar ta shaida cewa wadanda suka yi garkuwa da Cif Nwankwo sun ce a biya N200m. Daga baya sai suka rage kudin zuwa N12m.
Ana tsakiyar haka sai aka ji labari Sarkin na Isiala Umudi ya bar hannun wadanda suka sace shi, yanzu yana gidansa yana sararawa.
Yadda abin ya faru a jeji
Wanda ya san abin da ya faru, ya shaidawa manema labarai cewa Sarkin ya gudu ya bar wayoyin salularsa biyu a wajen ‘yan bindigan.
Blueprint ta rahoto Sarkin yana cewa ya sulale ne yayin da barci ya dauke mutanen, wani daga cikinsu kuma ya tafi shan tabar wiwi.
“Da rahamar Ubangiji, Mai martaba ya kubuta daga wajen miyagun ‘yan bindigan suka yi garkuwa da shi.
Ya yi amfani da sakacin ‘yan bindigan a dajin Okwu a karamar hukumar Ikeduru, ya tsere. Da taimakon Ubangiji ya samu agaji, yanzu yana gida.”
- Na kusa da Mai martaba
Jaridar ta tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Imo domin jin abin da ke faruwa, said ai kuma ba a samu jin ta bakin Micheal Abattam ba.
An sace Sarki a idon jama'a
A baya kun ji cewa labari mara dadi ya zo mana na yadda masu garkuwa da mutane sun dauke Mai martaba Eze Jewel Ndenkwo a ofis.
Tun da abin ya faru, sai da aka shafe fiye da sa’a 24 ba a ji ‘yan bindigan sun tuntubi ‘yanuwan Basaraken kamar yadda al’adarsu take ba.
Asali: Legit.ng