Yanzu Yanzu: Mahaifiyar Gwamna Akeredolu Ta Kwanta Dama

Yanzu Yanzu: Mahaifiyar Gwamna Akeredolu Ta Kwanta Dama

  • Mahaifiyar Gwamna Akeredolu na jihar Ondo, Lady Evangelist Grace Bosede Akeredolu JP, ta kwanta dama
  • Gwamnan ne ya sanar da labarin mutuwar mahaifiyar tasa a safiyar Alhamis, 15 ga watan Satumba
  • Ya bayyana cewa za su sanar da tsare-tsaren jana’izar marigayiyar wacce ta mutu a cikin baccinta

Ondo Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi babban rashi na mahaifiyarsa, Lady Evangelist Grace Bosede Akeredolu JP, a safiyar yau Alhamis, 15 ga watan Satumba.

Gwamnan na jihar Ondo ne ya sanar da labarin mutuwar mahaifiyar tasa a wata wallafa da ya yi shafinsa na Facebook.

Akeredolu da mahaifiyarsa
Yanzu Yanzu: Mahaifiyar Gwamna Akeredolu Ta Kwanta Dama Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa mahaifiyar tasa ta mutu cikin sauki a baccinta kuma cewa za su sanar da tsare-tsaren jana’izarta.

Wani bangare na rubutunsa na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi

“Cike da nadama da mika wuya ga Ubangiji, Ni da yan uwana muna sanar da batun mutuwar mahaifiyarmu, Lady Evangelist Grace Bosede Akeredolu JP, a safiyar yau. Ta mutu cikin sauki a baccinta.”

Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi

A wani labari na daban, wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Prince Tajudeen Olusi, ya gargadi masu zolayar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, kan lafiyarsa.

Olusi ya bayyana cewa babu wani dan adam da baya da wata matsala ta rashin lafiya da ke damunsa a rayuwa.

Da yake jawabi a wata hira da jaridar Daily Independent a ranar Talata, Olusi, ya ce duba da yadda Tinubu ke yawo a fadin kasar tun bayan da ya lashe tikitin APC ba tare da ya kwanta ba ya nuna babu abun da ya samu lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yar Najeriya ta shiga tashin hankali bayan yiwa sarauniyar Ingila mummunan fata

Asali: Legit.ng

Online view pixel