Ido Zai Raina Fata: ‘Yan Majalisar Dattawa Sun Fara Bincike A Kan Barayin Mai

Ido Zai Raina Fata: ‘Yan Majalisar Dattawa Sun Fara Bincike A Kan Barayin Mai

  • An kafa wani kwamiti a majalisar dattawa da zai yi bincike a kan satar danyen man fetur a Najeriya
  • Wannan kwamiti ya ziyarci yankin Neja-Delta domin ganewa idanunsa a kan duk satar mai da ake yi
  • Shugaban kwamitin, Sanata Bassey Akpan ya zanta da ‘yan jarida da suka sauka a filin jirgi na Ribas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Kwamitin majalisar dattawa da aka kafa domin binciken satan danyen man fetur a Najeriya yace ya soma bincike kan wannan aiki da aka ba shi.

Punch tace shugaban kwamitin majalisar, Sanata Bassey Akpan ya bayyana wannan a lokacin da suka zanta da manema labarai a filin tashin jirgi na Fatakwal.

Bassey Akpan yake cewa ana satar danyen man Najeriya, ana saida su a kasashen ketare. Wannan ya jawo kasar ta gagara hako adadin man da OPEC ta yanke.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abubuwan da Zan Yi a Kwanaki 100 na Farko da Zan Yi a Ofis

Sanatan ya shaidawa ‘yan jarida cewa ba za ta yiwu a iya tace mai a Najeriya idan har akwai bata-garin da suke sace danyen mai, suna saidawa a ketare ba.

Kwamitin Akpan zai ganewa idanunsa

“Niyyarmu ita ce mu ziyarci duk wata tashar mai a Neja Delta domin ganewa idanunmu, mu gano dalilin satar danyen mai, da dalilin asarar da ake yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mu a majalisar tarayya mun yi imani idan ana fasa kwaurin mai ko asarar danyen fetur, ba zai taba yiwuwa a iya tace danyen man fetur a gida ba.
Majalisar Dattawa
‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya Hoto: @NgrSenate
Asali: UGC

“Mun yarda akwai yadda kasar nan za ta rage wannan asara, saboda haka aikinmu ba na wasa ba ne.”

Zanga-zangar ma'aikata tayi tasiri

Rahoton da gidan talabijin Channels TV ya fitar a jiya, ya nuna cewa ‘yan majalisar sun kai wannan ziyara ne bayan wasu ma’aikatan mai sun fara zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno: An Zargi Shugaban Matasa da Fifita Yarbawa a Taron Jam’iyyar APC

A makon da ya gabata, ‘yan kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da gas ta Najeriya suka bukaci a kawo karshen satar danyen mai da ake yawan yi a kasar.

Hukumar NUPRC tace abin da ake hakowa a duk rana bai wuce ganguna 972,394 ba. Wannan ne mafi karancin danyen fetur da aka taba hakowa a shekaru 25.

A binciken da Sanatocin kasar za su gabatar, ana sa ran a bankado abin da ke faruwa, sannan a gabatarwa gwamnatin tarayya da shawarwarin da za a dauka.

INEC tayi waje da mutum miliyan 1.2

A wani bangaren, mun samu labari kwamishinan yada labarai na INEC mai gudanar da zabe a kasa yace sun yi fatali da sunaye 1,126,359 daga cikin rajistar zabe.

Da alama wasu daga cikin mutane 2,523,458 wadanda suka yi rajistar sabon katin zabe sun taba yi rajistar a baya, wannan ya sa ba za su samu katin PVC ba.

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

Asali: Legit.ng

Online view pixel