Abin da Ya Sa INEC ta Cire Mutane Fiye da Miliyan 1.1 Daga Cikin Rajistar Zabe

Abin da Ya Sa INEC ta Cire Mutane Fiye da Miliyan 1.1 Daga Cikin Rajistar Zabe

Hukumar INEC mai gudanar da zabe ta bayyana halin da ake ciki wajen rajistar masu neman PVC

An yi sabon rajistar katin PVC domin wadanda suka cika shekara 18 da suke shirin kada kuri’a a 2023

An yi amfani da na’urar ABIS wajen cire sunayen wadanda bai kamata sunayensu ya fito a rajista ba

Abuja - Hukumar INEC mai zaman kanta ta bayyana cewa ta cire sunayen mutane 1,126,359 daga rajistar wadanda suka nemi katin zabe a Najeriya.

Daily Trust tace daga cikin mutum 2,523,458 da suka yi rajista tsakanin 28 ga Watan Yunin 2021 zuwa 14 na Junairun 2022, an cire mutum 1,126,359.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na INEC, Festus Okoye ya bayyana wannan yayin da ya zanta da 'yan jarida a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili

Okoye yace tun karshen Yulin 2022 ake cire sunayen wasu da suka yi rajista da na’urar ABIS.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadannan mutane kurum za a sa sunansu a cikin wadanda za su samu damar kada kuri’a a zaben 2023, wanda yake zuwa nan da ‘yan watanni.

“Kafin nan, hukumar (INEC) ta sanar da mutanen Najeriya cewa daga cikin mutane 2,523,458 da suka yi sabon rajista, an goge sunayen 1,126,359.
INEC.
Hukumar INEC Nigeria Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Rajistar wadannan mutane ba tayi daidai ba, saboda haka an cire sunayensu.”

- Festus Okoye

Rahoton yace hakan yana nufin a wadanda suka nemi a ba su sabon katin zabe a Najeriya, mutane 1,397,099 ne kadai hukumar INEC za ta buga katinsu.

Automated Biometric Identification System

Na’urar Automated Biometric Identification System wanda ake kira da ABIS tana taimakawa wajen gano wadanda suka yi rajistar PVC fiye da sau daya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Buɗe Wa Jami'an 'Yan Sanda Wuta, Rayuka Sun Salwanta

A cikin kananin lokaci irin wadannan na’urori suna amfani da fasahar zamani ta hanyar bibiyar zanen hannuwa da fuskokin wadanda aka yi wa rajista.

Hukumar zaben tace tun ranar 31 ga watan Yulin 2022 aka dakatar da yin sabon katin PVC.

Mu na maraba da su Wike - Adeyemi

Ku na da labari PDP tana fama da rikicin cikin gida a wani bangaren saboda ‘dan takaranta ya fito daga Arewa, yankin da yake rike da mulki tun 2015

Sanata Smart Adeyemi wakilin yammacin jihar Kogi yana neman yayi amfani da damar rigingimun PDP domin yayi zawarcin Gwamna Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng