Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili

Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili

  • Kasar Amurka ta ayyana neman wani dan Najeriya, Chidozie Collins Obasi, ruwa a jallo kan zambar $30m
  • Hukumar bincike ta FBI ta bayyana cewa ana tuhumar Obasi kan damfarar jihar New York kudi fiye da dala miliyan 30 a matsayin mai siyar da na’urar hura iska a lokacin annobar korona
  • Hukumar ta FBI ta ci gaba da cewa wanda ake zargin ya damfari Amurkawa ne ta hanyar wani sakon imel wanda ke ba da ‘aiki daga gida’ na bogi

Rahotanni sun kawo cewa kasar Amurka na neman wani matashi dan Najeriya, Chidozie Collins Obasi, mai shekaru 29 ruwa a jallo kan zargin zambar kudade.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ana zargin dan Najeriyan da damfarar asibitocin Amurka kudi har dala miliyan 31 ta hanyar tallata na’urorin hura iska na korona wadanda babu su.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Matashi da FBI
Amurka Na Neman Wani Dan Najeriya Ruwa A Jallo, Ta Bayyana Dalili Hoto: Vanguard, businessday.ng, Getty Images
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga sashin shari’a na Amurka a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata wannan ta’asar ne daga Najeriya da taimakon abokan harkallarsa na kasar waje a tsakanin Satumban 2018 da Yunin 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana zargin Obasi da sauran abokan damfararsa sun samu fiye da $31,000,000 ta wannan hanya, inda yawancin kudaden suka fito daga jihar New York.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Ana zargin Obasi ya hada kai da wani dilallin kayan asibiti a Amurka don siyar da wadannan na’urorin hura iska da babu su, sannan ya yaudari jihar New York wajen tura diyar da dala miliyan 30 na siyan na’urorin da babu su.”

A cewar takardar tuhumar, Obasi wanda ya tsere a halin yanzu, yana fuskantar tuhuma na hada kai wajen aikata zamba ta hanyar sako, tuhume-tuhume shida na sakon zamba da wasu tuhume-tuhume 16 na zamba.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

Yana fuskantar daurin shekaru 621 a gidan yari, sakin shekaru biyar karkashin kulawa, da kuma tarar $5,750,000 kuma za a bukaci ya mayar da sama da $31,000,000 da ya samu ta hanyar damfara idan aka same shi da laifi, rahoton The Cable.

Abdullahi Haske: Matashin Biloniya Daga Jihar Adamawa Wanda Ba Kowane Ya Sansa Ba

A wani labari na daban, Allah ya albarkaci Najeriya da al’umma masu kwazo da jajircewa wajen neman na kai. Da yawa daga cikin wadannan yan Najeriya sun tara arzikin da har sun kai matakin biloniya.

Abdullahi Haske na daya daga cikin irin wadannan mutane sai dai sam shi yana tafiyar da lamuransa ne cikin sauki ba tare da nuna shi din wani mai arziki bane.

Ko shakka babu, Haske mai shekaru 35 na daya daga cikin matasa biloniya a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel