Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura

Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura

  • NCC ta shawarci ‘yan Najeriyan dake amfani da wasu manhajojin 'Google Chrome Extension' guda biyar da su gaggauta goge su
  • Hukumar ta NCC ta yi gargadin cewa, an kirkiri wadannan manhajoji ne domin su saci bayanan jama'a haka siddan
  • Abin ban mamakin ma shi ne, manhajojin da NCC ta lissafa ba sabbi bane, domin kuwa sama mutane miliyan daya ne suka daukesu a na'urorinsu

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwar ta Najeriya ta gano wasu abubuwan da ka iya kawo tsaiko ga 'ya kasa a kan manhajar Google Chrome.

A cewar hukumar, irin wadannan manhajoji na bin diddigin duk wasu shafuka da mai amfani dasu ke bi.

NCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin yanar gizo, wanda Legit.ng ta gani.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Jihar Kogi Ta Gudanar Da Jana'izar Mutane 130 Da Babu Masu Shi

NCC ta gargadi 'yan Najeriya kan wasu manhajoji
Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura | Hoto: ncc.gov.ng
Asali: Facebook

Manhajojin guda biyar da NCC tace 'yan su gujewa

  1. McAfee Mobile
  2. Netflix Party/Netflix Party 2
  3. Full Page Screenshot Capture Screenshotting
  4. FlipShope Price Tracker Extension
  5. AutoBuy Flash Sales

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NCC ta yi gargadin cewa, duk da akwai mutum sama da miliyan 1.4 dake amfani da manhajojin, duk da haka akwai hadarori da ke tattare dasu idan ba a kula ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, NCC ta ce akwai manhajojhi da yawa da Google suka cire a ma'ajiyar manhajoji Web Store, to amma abu ne mai wahala iya tsaftace kafar ta yanar gizo.

A bangare guda, NCC ta shawarci masu amfani da wayoyin hannu da sauran abubuwan zamani da su ke karatun ta natsu kafin sauke manhaja a na'ur'rinsu.

Ana amfani da Chrome Extensions a na'urorin teburi da na tafi d agidanta, kana ana amfani da irin manhajojin da NCC ke gargadi a kai a wayoyin hannu.

Kara karanta wannan

Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa

An Datsi Tashar Yanar Gizon INEC Daga Asiya a Lokutan Zaben Gwamnan Jihar Ekiti da Osun

A wani labarin, akwai yiwuwar a samu matsala a babban zaben 2023 yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sabon tsaiko a shafinta na duba sakamakon zaben (IReV).

Wani tahoton TheCable ya ce, INEC ta bude sirri, tace wasu madatsa daga nahiyar Asiya sun datsi tashar duba sakamakon zabe a zabukan da suka kammala na jihohin Ekiti da Osun.

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ne ya bayyana wannan lamari a yau Juma'a 9 ga watan Satumba a Abuja yayin da yake magana a wani taron da ya shafi jami'an sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel