Wurin neman kiba: Bidiyon yadda aka lalatawa budurwa fuska daga zuwa gyaran fata

Wurin neman kiba: Bidiyon yadda aka lalatawa budurwa fuska daga zuwa gyaran fata

  • Kyakyawar budurwa mai farar fata ta bayyana damuwarta bayan gyaran fatan da taje tayi ya mayar da ita baka kuma mummuna
  • A bidiyonta na baya da ta nuna, fatarta fes amma ta garzaya domin kara ingantata, lamarin da ya bar ta da nadamar yadda ta koma
  • A washegarin da tayi gyaran fatar, ta fara baki inda wasu kuraje masu muni suka cika mata fuska, kwanaki 7 bayan nan kuwa abun ya kazanta

Wata budurwa ta koka da yadda fuskarta ta koma tamkar an yi gobara bayan ta je gyaran fata da kuma neman karin kyau.

Budurwar mai farar fata ta koma baka inda wasu kuraje masu muni da bada takaici cika mata kyakyawar fuskarta bayan taje tayi gyaran fata.

Skin irritation
Wurin neman kiba: Bidiyon yadda aka lalatawa budurwa fuska daga zuwa gyaran fata, Hoto daga TikTok/@achalang_baby
Asali: UGC

Ta fara da wallafa tsofaffin hotunan ta masu kyau inda take bayyana fuskarta babu kurji ko daya amma daga bisani canjin da aka samu ya fusatata.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

Daga nan ta wallafa bidiyo mai dauke da lokacin da aka fara gyaran fuskar, wanda a tunaninta zai inganta mata fata tare da fitar da ita fes, lamarin da bata san zai kunyatata ba tare da barinta da takaici.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta sanar da cewa, tun washegarin ranar da aka yi mata gyaran fatar fuskar ta rine tare da komawa baka, kuraje suka fara fito mata. Abun ya kazanta bayan kwanaki bakwai da yin gyaran fuskar, har ta kai ga fushi yasa ta aske gashin kanta.

Ga bidiyon a nan.

Budurwa ta sha da kyar a hannun danginta bayan ta haifo balaraben jariri bayan ta dawo daga Saudiyya

A wani labari na daban, masoyan wata mata a Kenya sun taimaketa bayan 'yan uwanta dake Siaya su fatattake sakamakon haihuwar balaraben jariri da tayi bayan ta dawo daga Saudiyya.

Kara karanta wannan

Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki

Anna Awuor mai shekaru 29 a duniya ta shiga wani hali bayan danginta sun gujeta tare da jaririn da ta haifa bayan ta dawo daga Saudi Arabia.

Kamar yadda mai taimakon jama'a, Judy Oricho ta bada labarin halin da matar ta shiga a shafinta na Facebook, ubangidan Anna na Saudi Arabia ne ya ci zarafinta kuma sakamakon hakan ta samu juna biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng