Safarar bindigogi: Shekara 12 kenan ana shigo da makamai ta barauniyar hanya - DSS
- An dade ana shigo da muggan makamai kasar nan
- Wannan shine babban musabbabin yawaitan fashi da makami a Najeriya
Hukumar tsaron leken asiri, DSS, jiya, ta bayyanawa babban kotun Najeriya da ke zaune a Legas cewa daya daga cikin wanda aka damke da shigo da makamai 661 a watan Junairu 2017, ya kai shekara 12 yana shigo da makamai cikin Najeriya.
Shugaban binciken hukumar DSS, Mr. Wale Odu, yayinda yake bayani a gaban kotun Jastis Ayotunde Faji, lokacin da ake gurfanar da mutane biyar da suka shiga hannu da laifin shigo da bindigogi 661 cikin Najeriya ta barauniyar hanya, yace ya tattauna da su sosai yayin gudanar da binciken sa.
Zaku tuna cewa a ranan 14 ga watan Yuni, 2017, hukumar Kwastam ta gurfanar da jam’ianta 2 Muhmud Hassan da Salisu Abdulahi Danjuma, tare da wasu Oscar Orkafor, Donatus Ezebunwa Achinulo da Matthew Okoye a gaban Jastis Ayotunde Faji a ka laifin shigo da makamai, rufa-rufa, samar da takardun bogi, baiwa jami’an gwamnati cin hanci da shigo da haramtattun kayayyaki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng